Ana Jiran Ya Dawo da Tallafi, Tinubu Ya Aika da Sako Mai Zafi ga Masu Zanga Zanga

Ana Jiran Ya Dawo da Tallafi, Tinubu Ya Aika da Sako Mai Zafi ga Masu Zanga Zanga

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu zanga-zanga da su haƙura da ita su zo a tattauna domin a samu mafita
  • Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne ga matasan da suka fito kan tituna domin nuna adawa da halin ƙuncin da ke ciki a yayin jawabin da ya yi ranar Lahadi
  • Shugaban ƙasan ya kuma jajantawa waɗanda suka rasa ƴanuwansu a sakamakon zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zanga-zangar #Endbadgovernance da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da su gaggauta dakatar da zanga-zangar su fito domin a tattauna.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi makudan kudaden da ya ba jihohi domin talaka ya samu sauki

Tinubu ya bukaci a dakatar da zanga-zanga
Tinubu ya bukaci masu zanga-zanga su hakura Hoto: @harmless1234, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya yiwa ƴan Najeriya jawabi

A wani jawabi da ya yi a ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya ce ya ji takaicin asarar rayuka da dukiyoyi a zanga-zangar da ake ci gaba da yi, inda ya buƙaci masu yin ta da su tsagaita wuta, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu wanda ya jajantawa waɗanda suka rasa rayukansu da iyalansu, ya ƙara da cewa ya zama wajibi a tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Tinubu ya yi gargaɗi

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya ta zura ido ta bari wasu ƴan tsiraru masu wata manufa ta siyasa su wargaza ƙasar nan ba.

"A matsayin shugaban ƙasar nan, dole ne na tabbatar da zaman lafiya. Bisa rantsuwar da na yi domin kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa, gwamnatinmu ba za ta zura ido ta bari wasu tsiraru masu manufar siyasa su wargaza ƙasar nan ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ba zai lamunta ba a Najeriya

"A bisa dalilin hakan, ina kira ga masu zanga-zanga da masu shirya ta da su dakatar da ita tare da zuwa a tattauna domin kodayaushe a shirye na ke kan hakan."
"Najeriya na buƙatar mu haɗa ƙarfi da ƙarfe ba tare da la'akari da shekaru, jam'iyya, ƙabila, addini ko wasu abubuwan ba, domin mu ciyar da ƙasarmu gaba."

- Bola Ahmed Tinubu

Lauya ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa lauyan kare haƙƙiin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya bayyana abin da ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi domin shawo kan matasa masu zanga-zanga.

Dubunnan ƴan Najeriya da suka fusata ne suka fito manyan biranen ƙasar nan domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng