Zanga Zanga: Daga Karshe Tinubu Ya Sanya Lokacin Yin Jawabi ga 'Yan Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan
- Shugaba Tinubu zai yi jawabin ne na kai tsaye ga ƴan al'ummar Najeriya da ƙarfe 7:00 na safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Agustan 2024
- Dubunnan matasa ne dai suka fito kan tituna domin nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙi da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabin kai tsaye ga ƴan Najeriya a ranar Lahadi, 4 ga watan Agustan 2024.
Shugaban ƙasan zai gudanar da jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar ranar Lahadi.
Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar da yammacin ranar Asabar, 3 ga watan Agustan 2024, a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai yi jawabi ga al'ummar Najeriya a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024 da misalin ƙarfe 7:00 na safe."
"Gidajen talbijin, rediyo da sauran kafafen watsa labarai su kama tashar NTA da gidan rediyon Najeriya (FRCN) domin jawabin."
"Za a maimaita jawabin a tashoshin NTA da FRCN da ƙarfe 3:00 na yamma da ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Lahadi."
- Ajuri Ngelale
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Rana ta 3: Jami'an tsaro sun cafke 'yan Najeriya da masu zanga-zanga
- Zanga zanga: Duk da barkewar rikici, gwamna ya fadi dalilin kin kulle mutane a gida
- Babban lauya ya ba Tinubu lakanin kawo karshen zanga zangar da ake yi
Uba Sani ya caccaki jagororin zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya caccaki masu shirya zanga-zangar #EndBadGovernance a jihar bisa zargin ƙin fitowa su jagoranci zanga-zangar.
A cewar Uba Sani, maimakon su jagoranci zanga-zangar, sai suka fake suka bar matasa marasa galihu su jagoranci zanga-zangar.
Asali: Legit.ng