Gwamna Ya Fito Ya Fadi Babban Kuskuren Masu Shirya Zanga Zanga
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya fito ya nuna takaicinsa kan rashin fitowar da masu shirya zanga-zanga suka yi a jihar
- Gwamnan ya nuna rashin fitowa su jagoranci zanga-zangar kuskure ne domin hakan ya jawo wasu ɓata gari sun yi amfani da ita wajen yin sata
- Ya nuna cewa su a baya da suka jagoranci zanga-zanga, ba su bari an kama wasu ba, su kawai aka kama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya caccaki masu shirya zanga-zangar #EndBadGovernance a jihar bisa zargin ƙin fitowa su jagoranci zanga-zangar.
A cewar Uba Sani, maimakon su jagoranci zanga-zangar, sai suka fake suka bar matasa marasa galihu su jagoranci zanga-zangar.
Gwamnan, ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da gidan jaridar BBC Hausa a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Uba Sani ya ce kan zanga-zanga?
Gwamna Uba Sani ya ce idan masu shirya zanga-zangar na kusa da sun gargaɗi matasan da suka yi amfani da zanga-zangar wajen yin sata.
"Mu a baya da muka fito muka jagoranci zanga-zanga an kama mu. Ba mu taɓa bari a kama matasa da sauran jama’a da suka fito zanga-zanga tare da mu ba. Mu ne aka kama."
"Idan kuna kiran a fito zanga-zanga, ku ne ya kamata ku yi kan gaba wajen fitowa. Suna ta magana a shafukan sada zumunta, amma ba su fito a lokacin zanga-zangar ba."
"Da a ce suna nan, da za ta fi kyau domin aƙalla, da sun gargaɗi matasan da ke fasa shagunan jama’a da wawashe dukiyar jama’a, amma ba su fito ba, ƴaƴansu ba su fito ba. Ƴaƴan talakawa ne suka fito yayin zanga-zangar. Ina ganin hakan bai dace ba."
- Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya zargi ƴan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi zargin cewa ƴan adawa na amfani da zanga-zangar da ake yi domin ɗaukar fansar kashin da suka sha a zaɓen 2023.
Gwamnan ya yi iƙirarin cewa wasu ƴan adawa ne ke tunzura matasa da sauran talakawa su shiga zanga-zangar da aka fara ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng