Sarki Muhammadu Sanusi II Ya Fadi Abin da Za Ayi da Kayan 'Ganimar' Zanga Zanga
- Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya yi takaicin yadda zanga-zangar lumana ta rikide a jihar zuwa sace-sace
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce mummunar dabi'ar da aka gani ta sace-sacen kayan jama'a bai yi dadi ba
- Ya shawarci mazauna jihar da su guji sayen duk wani kaya da aka tabbatar a lokacin zanga-zanga aka sato shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi Allah wadai da mummunan halin sace-sace da aka yi a lokacin zanga-zanga.
Duk da da farko an fara zanga-zangar lumana a jihar Kano cikin kwanciyar hankali, amma da rana ta bude sai aka fara wasoson kayan jama'a.
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa sarkin ya shawarci mazauna jihar su guji sayen kayayyakin da aka sata a lokacin zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a sun gudanar da zanga-zanga cikin tashin hankalin a ranar farko na fitowa domin nuna adawa da manufofin Bola Ahmed Tinubu.
"A ba wa 'yan sanda bayani," Sarki Sanusi II
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nemi jama'ar jihar su gaggauta mika bayanan kayan sata da aka dauka lokacin zanga-zanga ga 'yan sanda.
Arise News ta tattara cewa Sarki Sanusi ya fadi haka ne ga iyaye da sauran jama'ar gari a kokarinsa na ganin an hana sayen kayan sata a jihar
Sarkin ya roki wadanda su ka yi sace-sacen su kai kayan da su ka sata zuwa ga jami'an tsaro, domin hakan ne zai fi dacewa.
'Yan sanda sun fara neman kayan 'ganima'
A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta fara binciken gidajen jama'a da ake zargi da kwashe kayan jama'a yayin zanga-zanga a ranar Alhamis.
An gano jami'an su na bin gidaje domin karbo kayan da zummar mayarwa ga masu su, yayin da ake ci gaba da dokar hana fita a fadin jihar.
Asali: Legit.ng