Kungiyar NLC Ta Dakatar da Zanga Zanga? Gaskiya Ta Bayyana
- Ƙungiyar NLC ta sake nanata cewa ba ita ce ta shirya zanga-zangar adawa da halin ƙuncin da ake fama da shi wacce ake gudanarwa a faɗin ƙasar nan
- NLC ta fitar da wata sanarwa inda ta musanta cewa ba ta dakatar da zanga-zangar da ake gudanarwa ba a faɗin ƙasar nan
- Dubunnan mutane ne suka fito kan tituna a biranen Najeriya a zanga-zangar nuna adawa da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da wahalar da ake sha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta dakatar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Ƙungiyar NLC ta kuma musanta cewa ta sake matsayarta kan zanga-zangar wacce ake yi a faɗin ƙasar nan.
A wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Juma’a, 2 ga watan Agusta a shafinta na X, ƙungiyar ta NLC ta musanta rahotannin cewa ta dakatar da zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsayar NLC kan zanga-zanga
A watan Yuli ne ƙungiyar NLC ta bayyana cewa ba ita ce ta shirya zanga-zangar adawa da halin ƙunci a faɗin ƙasar nan ba.
A lokacin, ƙungiyar ta mayar da martani ga rahotannin da ke cewa ta janye daga shiga zanga-zangar ta ƙasa.
A ranar Juma’a, 2 ga Agusta, 2024, rahotanni daban-daban guda biyu sun bayyana.
Wani rahoton ya yi iƙirarin cewa ƙungiyar kwadago ta sanar da dakatar da zanga-zangar, yayin da wani kuma ya ce NLC ta sake duba matsayarta kan zanga-zangar.
Wane martani NLC ta yi?
Yanzu dai ƙungiyar NLC ta mayar da martani a hukumance kan wannan jita-jita.
NLC ta bayyana cewa jita-jitar da ake yaɗawa maganar da ta yi ne a lokacin da aka fara shirin zanga-zanga, inda ta ba gwamnati shawara domin ta tattauna da masu shirya ta.
Ta bayyana cewa har yanzu tana kan wannan matsayar na ganin gwamnati ta tattauna da masu zanga-zangar domin hakan shi ne mafita.
Lauya ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa lauyan kare haƙƙiin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya bayyana abin da ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi domin shawo kan matasa masu zanga-zanga.
Dubunnan ƴan Najeriya da suka fusata ne suka fito manyan biranen ƙasar nan domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki.
Asali: Legit.ng