Rana Ta 3: Masu Zanga Zanga Sun Yi Takansu Yayin da Jami'an Tsaro Suka Buɗe Wuta
- Yan sanda sun buɗe wuta a saman iska tare da fesa hayaƙi mai sa hawaye da suke tarwatsa tsirararun masu zanga-zanga a Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zanga sun sake komawa filin wasa na Moshood Abiola amma sun fuskancin fushin ƴan sanda
- Yau Asabar, 3 ga watan Agusta, 2024 ta zama ita ce rana ta uku da fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati mai ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - 'Yan sanda sun tilastawa wasu tsirarun masu zanga-zanga kan halin ƙuncin da ake ciki, ficewa daga filin wasa na Moshood Abiola da ke birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun sake komawa filin wasan bayan da fari sun kaurace wa filin a safiyar yau Asabar, 3 ga watan Agusta, 2023.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, masu zanga zangar sun koma filin wasan ɗauke da tutoci da kwalaye masu rubutu daban-daban a rana ta uku da farawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ƴan sandan da aka girke a filin sun yi harbe-harbe a kan iska domin tarwatsa tawagar masu zanga-zangar, sannan suka harba masu hayaki mai sa hawaye.
Ƴan sanda sun buɗe wuta
Nan take dai suka tarwatse inda wasu daga cikin tsirararun masu zanga-zangar suka hau motocinsu suka bar wurin, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Duk da ƴan sanda sun kori matasan da suka fito zanga zanga da ƙarfi da yaji a Abuja, amma ana ganin bai kamata a tarwatsa su a wurin da aka amince su yi amfani da shi ba.
Yayin da ‘yan sandan suka kama masu zanga-zangar da ba su gudu ba, wasu jami’an tsaro sun fara harbi matasan da kuma ‘yan jarida masu ɗauko rahoto.
Tinubu ya kare matakan da ya ɗauka
A wani rahoton kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri da nufin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne ranar Jumu'a a Abuja a lokacin da ƴan Najeriya suka shiga rana ta biyu a zanga-zangar da suka fara.
Asali: Legit.ng