Babban Lauya Ya Ba Tinubu Lakanin Kawo Karshen Zanga Zangar da Ake Yi

Babban Lauya Ya Ba Tinubu Lakanin Kawo Karshen Zanga Zangar da Ake Yi

  • Inibehe Effiong ya yi magana kan zanga-zangar da matasa suka fito suna yi a faɗin ƙasar nan saboda tsadar rayuwa
  • Lauyan na kare haƙƙin ɗan Adam ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sairari buƙatun da masu zanga-zangar suka gabatar
  • Ya yi nuni da cewa daga cikin abin da ya kamata Tinubu ya yi ciki har da rage yawan ministocin da ke cikin gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Lauyan kare haƙƙiin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya bayyana abin da ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi domin shawo kan matasa masu zanga-zanga.

Dubunnan ƴan Najeriya da suka fusata ne suka fito manyan biranen ƙasar nan domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Wani malamin addini ya gayawa Tinubu gaskiya, ya fadi babbar matsalar gwamnatinsa

Lauya ya ba Shugaba Tinubu shawara
Inibehe Effiong ya bukaci Tinubu ya saurari bukatun masu zanga-zanga Hoto: @InibeheEffiong
Asali: Twitter

Inibehe Effiong, yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Juma'a, ya ce kamata ya yi Shugaba Tinubu ya saurari buƙatun masu zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka da cewa har yanzu hukumomin Najeriya ba su dauƙi alhakin kashe masu zanga-zangar #EndSARS a shekarar 2020.

Wace shawara lauya ya ba Tinubu?

"Kafin mu farka a gobe, ina son na ji Shugaba Tinubu ya sanar da ƴan Najeriya cewa ya rage adadin ministocinsa zuwa 37."
"Ina son na ji Tinubu ya sanar da cewa an rage kuɗaɗen da ake kashewa a gwamnati da aƙalla kaso 50% cikin 100%.
"Ina so na ji cewa majalisar tarayya da shugaban ƙasa sun sanar da cewa an rage kuɗaɗen da ake kashe a majalisar an rage su da kaso 50%."
"Ina so na ji cewa Tinubu ya sanar da rage farashin man fetur sannan an rage kuɗin wutar lantarki."

Kara karanta wannan

Duk da katobarar da ya yi, Akpabio ya sake neman wata bukata wajen 'yan Najeriya

- Inibehe Effiong

Fasto Ayodele ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara.

Babban malamin addinin ya shawarci Shugaba Tinubu da ya kori ministoci da hadimansa saboda suna da matsala ga gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng