Ana Cikin Zanga Zanga, Rundunar Sojoji Ta Sanar da Kashe Miyagu Sama da 500 a Najeriya
- Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun samu nasarar halaka ɗaruruwan ƴan ta'adda a watan Yuli
- Sojojin dai sun ci gaba da kai hare-haren kan miyagun ƴan ta'adda da sauran masu aikata manyan laifuka a sassan ƙasar nan
- Bayan ƙashe yan ta'adda sama da 500, sojojin sun kuma ceto mutane 479 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 572 a watan Yulin da ya gabata a Najeriya.
Haka nan kuma gwarazan jami'an sojojin sun kuma cafke wasu miyagun ƴan bindiga da ƴan tada ƙayar baya 790 a wannan wata da ake magana a kansa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito hedkwatar tsaron na cewa dakarun sun kuɓutar za mutane 479 daga hannun masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun DHQ na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka cikin farin ciki a taron manema labarai a Abuja ranar Jumu'a, This Day ta rahoto.
Sojoji sun kwato muhimman abubuwa
Janar Buba ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci (watan Yuli), dakarun sojojin sun kwato danyen mai da aka sace, wanda aka kiyasta ya haura Naira biliyan uku.
"A watan Yulin 2024, sojoji sun kashe 'yan ta'adda 572, sun kama 790 da ake zargi da aikata ta'addanci da wasu miyagun laifuka, tare da ceto mutane 479 da aka yi garkuwa da su.
"Bugu da kari, sojojin sun kwato makamai 440, alburusai 10,589 tare da daƙile satar ɗanyen man da aka kiyasta ya kai na kimanin N3,652,382,080.00.
"Dakarun sojoji ba za su yi ƙasa a guiwa ba za su ci gaba da zage dantse a aikinsu na kare martabar Najeriya."
Yan bindiga sun sace kantoma a Kogi
Kuna da labarin ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi, Barista Zacchaeus Dare Michael tare da wasu hadimai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga sun tare kantoman a kan titin Kabba zuwa Okene, sannan suka tafi da shi zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng