Rana ta 3: Gwiwar Masu Zanga Zanga Ta Fara Sanyi, Jama'a Ba Su Fito a Abuja ba
- A yau Asabar ne aka shiga rana ta uku daga cikin kwanaki 10 da za a gudanar da zanga-zanga a Najeriya
- 'Yan kasar nan sun fusata biyo bayan matsin rayuwa da su ke ganin manufofin shugaba Bola Tinubu ne ya jawo
- Sai dai a yau, jama'a ba su fito sosai a babban birnin tarayya Abuja ba inda ake sa ran ci gaba da zanga zanga domin tura sako ga shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwiwar jama'a ta fara sanyi yayin da aka samu karancin masu ci gaba da zanga-zanga a rana ta uku a baban birnin tarayya Abuja.
Kwanaki 10 cir 'yan kasar nan su ka bayyana cewa za su yi su na zanga-zangar lumana ta nuna rashin jin dadin manufofin shugaba Bola Tinubu.
A labarin da ya kebanta da Daily Trust, an tabbatar da cewa mutane ba su yi fitowar da aka yi a kwanaki biyun farko na zanga-zanga ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko mutum 1 babu da sunan zanga-zanga
Ko mutum daya ba a gani a filin wasan Abuja a ranar Asabar ba yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da rangadi tun da har yanzu ana cikin kwanaki 10 zanga-zanga.
An gano 'yan sanda da 'yan jarida sun yi cirko-cirko su na jiran abin da zai faru domin akwai yiwuwar a fito ci gaba da zanga-zangar.
"Masu zanga-zanga na hutu," dan sanda
Daga cikin jami'an tsaron da ke tsaye su na kokarin tabbatar da tsaro a filin wasan Abuja ya yi shagube ga masu zanga-zanga.
Da ya juya ya kalli abokin aikinsa, dan sandan ya ce su masu zanga-zanga sun tafi hutun karshen mako.
Masu zanga-zanga sun fito a Jigawa
A wani labarin kun ji yadda jama'a a Jigawa su ka yi watsi da umarnin gwamnatin jihar na cewa kowa ya zauna a gida, inda su ka fito zanga-zanga.
Tun a rana ta farko aka samu wasu fusatattun matasa su ka kona ofishin jam'iyyar APC a jihar, inda aka samu rahotannin 'yan daba sun shiga lamarin.
Asali: Legit.ng