Shugabannin Zanga Zanga Sun Samu Matsala Bayan DSS Ta Dauki Wani Mataki

Shugabannin Zanga Zanga Sun Samu Matsala Bayan DSS Ta Dauki Wani Mataki

  • Wasu shugabannin da suka jagoranci zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci da rashin tsaro a jihar Katsina sun faɗa hannun hukumar DSS
  • Hukumar DSS ta gayyaci shugabannin ne zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi inda daga bisani suka tsare su
  • Hakan ya biyo bayan fara zanga-zangar da aka yi a ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024 a faɗin ƙasar nan kan taɓarɓarewar al'amura

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke jagororin zanga-zangar nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro da aka gudanar a jihar Katsina.

Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma, shugabannin zanga-zangar "Struggle for Good Governance" an gayyace su zuwa ofishin DSS da ke Katsina, inda daga bisani aka tsare su.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun dira gidan Buhari a Daura, bayanai sun fito daga Katsina

DSS sun cafke shugabannin zanga-zanga a Katsina
Hukumar DSS ta tsare shugabannin masu zanga-zanga a Katsina Hoto: @OfficialDSS
Asali: Facebook

DSS ta cafke jagororin zanga-zanga

Hakazalika, Mujittapha Usman, wanda ya jagoranci zanga-zangar a ƙaramar hukumar Malumfashi, shi ma jami’an tsaro sun kama shi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu abokan shugabannin da suka bayyana hakan sun ce hukumar DSS ta tuntuɓi mutanen ne ta wayar tarho da sanyin safiya, rahoton Katsina Times ya tabbatar.

Sun buƙaci su bayyana a ofishinsu domin amsa tambayoyi game da zanga-zangar da aka yi a ranar Alhamis.

Sai dai majiyar ta bayyana cewa da isar su hedkwatar DSS ta Katsina, an tsare su kuma har yanzu ba a sake su ba har zuwa wannan lokacin.

Zanga-zanga ta rikiɗe a Katsina

Zanga-zangar wacce aka fara cikin lumana ta riƙiɗe zuwa wani abu daban ne lokacin da wasu gungun mutane da suka haɗa da ƙananan yara, suka taru a titunan birnin Katsina ɗauke da sanduna da ganyayyaki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Hankula sun tashi bayan jami'in tsaro ya harbi kansa

Sun yi ta faɗin “Bama yi Bama yi” yayin da suke ƙoƙarin lalata kayayyakin jama’a.

Da farko dai masu zanga-zangar sun ƙona wata motar sintiri ta NSCDC a babban birnin jihar tare da ƙona ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Dutsinma.

Hakan ya sanya gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta tsawon awa 24 a birnin Katsina da ƙaramar hukumar Dutsinma.

Masu zanga-zanga a gidan Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu fusatattun masu zanga-zanga sun yi dafifi zuwa gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

Masu zanga-zangar waɗanda suke da yawa, sun shiga zanga-zangar #EndBadGovernance da aka fara a faɗin ƙasar nan ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng