Sarki Sanusi II Ya Yi Magana Yayin da Zanga Zanga Ta Ƙara Ɓarkewa a Kano
- Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga matasa su hakura da zanga zanga, kar su bari a yi amfani da su a ruguza Kano, Arewa da ƙasa baki ɗaya
- Sarkin Kano ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan labari ya ɓulla cewa wasu matasa sun sake fitowa zanga-zanga duk da an sa dokar kulle
- Sanusi II ya yi kira ga mazauna Kano da kar su bari a maimaita abin da ya faru jiya Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga matasa da ka da su bari a yi amfani da su a durkusar da Kano, Arewa da Najeriya.
Sarkin ya yi wannna kira ne da aka samu labarin cewa masu zanga-zanga sun koma kan tituna duk da dokar hana fita da aka sanya da nufin kwantar da tarzoma.
Masu zanga-zanga sun take dokar Gwamna
Daily Trust ta ruwaito yadda masu zanga-zangar suka sake haduwa a Tudun Wada da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano da yammacin ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun sake haduwa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sassauta dokar hana fita domin ba musulmi damar zuwa Masallacin Juma'a.
Bayan sauko wa daga masallacin Jumu'a, aka ga matasan na ƙara taruwa a gadar da ta haɗa iyakar Tudun Murtala da Tudun Wada.
Da yawa daga cikinsu suna rike da kwalaye, sannan suna rera waka da tafi, daga bisani suka fara tafiya bayan wani matashi ya yi musu jawabi.
Sarki Sanusi II ya lallashi matasa
A wani taron manema labarai da ya gudanar a fadarsa ta Gidan Rumfa, sarkin ya nuna damuwa kan yadda aka wawushe kayan gwamnati da na al'umma haka kurum.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce abin da ya faru a lokacin zanga-zanga babban koma baya ne ga jihar Kano, yankin Arewa da ma kasa baki daya, cewar The Nation.
“Ina kira ga al’ummar Kano da kada su bari a maimaita abin da ya faru jiya ko kuma a yaudare su su ci gaba da tayar da tarzoma,"
- Muhammadu Sanusi II
Sojoji sun yi magana kan zanga-zanga
Kuna da labarin Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Musa ya ce sojoji za su shiga tsakani idan masu zanga zanga suka ci gaba da keta doka.
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa idan su ka fahimci lamarin ya sha kan ƴan sanda, za su kawo ɗauki domin tabbatar da zaman lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng