Zanga Zanga: CUPP Ta Bayyana Babban Kuskuren da Zai Iya Jefa Tinubu a Matsala
- Yayin da matasa ke cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, kungiyar CUPP ta magantu
- Kungiyar CUPP ta bayyana babban kuskuren da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a kan zanga zangar da aka fara
- Haka zalika kungiyar ta yi kira na musamman ga jami'an tsaro kan yadda suke mu'amala da masu zanga zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta yi magana kan zanga zangar da matasan Najeriya suka fara.
CUPP ta caccaki shugaba Bola Tinubu kan rashin nuna kwarewa wajen magance lamarin zanga zangar tun a karon farko.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin kungiyar, Kwamared Mark Adebayo ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CUPP: 'Tinubu bai nuna kwarewa ba'
Kungiyar CUPP ta bayyana cewa Bola Tinubu bai nuna kwarewa wajen tunkarar zanga zangar ba saboda ko magana bai fito ya yi da kansa ba.
CUPP ta ce wani abin da ke nuna rashin kwarewa da kuskure shi ne yadda jami'an shugaban kasa suka rika maganganu da suka kara tunzura matasa.
Wa zai dauki alhakin wadanda aka kashe?
Vanguard ta wallafa cewa Kungiyar CUPP ta ce saboda halin ko in kula da gwamnatin tarayya ta yi a kan zanga zangar ya jawo mutuwar yan Najeriya ita za ta dauki alhaki.
CUPP ta ce ta fadi haka ne saboda gwamnatin ta samu dukkan damar daukan matakin hana zanga zangar amma ta yi biris.
Kiran CUPP ga jami'an tsaron Najeriya
Kungiyar ta yi kira ga jami'an tsaro su nuna mu'amala mai kyau da masu zanga zangar a dukkan jihohin Najeriya.
Haka zalika ta yi kira ga yan Najeriya da su kaucewa sace sace da dukkan ayyukan barna da sunan zanga zanga.
Zanga zanga: Jam'iyyar PDP ta yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa jami'yyar adawa ta PDP ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga zangar da ta barke.
PDP ta ambaci abubuwan da ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin kwantar da hankalin matasan da suke zanga zanga a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng