Rana Ta 2: Ƴan Sanda Sun Bude Wa Masu Zanga Zanga Wuta, Mutane da Yasa Sun Jikkata
- Masu zanga-zanga sun gamu da fushin ƴan sanda yayin da suka sake taruwa a kusa da babban asibitin ƙasa a birnin Abuja yau Jumu'a
- Matasan sun sake taruwa duk da kashedin da rundunar ƴan sanda ta yi bayan tayar da hargitsi a rana ta farko da suka fara zanga-zanga
- Ana fargabar mutum biyar sun jikkata lokacin da yan sandan suka yi harbe-harbe da fesa hayaki mai sa hawaye don tarwatsa matasan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ana fargabar masu zanga-zanga da dama sun samu raunuka yayin da ƴan sanda suka tarwatsa su a babban birnin tarayya Abuja yau Jumu'a.
Tun da safe dai masu zanga-zangar suka sake fitowa a rana ta biyu, inda suka taru a bayan babban asibitin ƙasa da ke Abuja duk da kashedin rundunar ƴan sanda.
Ƴan sanda sun yi kashedi kan zanga-zanga
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, tun farko rundunar ƴan sandan Abuja ta gargaɗi masu zanga-zangar cewa kar su fito saboda abubuwan da suka faru a ranar farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai masu zanga-zangar sun yi fatali da kashedin ƴan sanda, inda suka sake taruwa a kusa da babban asibiti na ƙasa yau Jumu'a, a rahoton The Cable.
Jami’an ‘yan sandan sun mamayi masu zanga-zangar a bayan Asibitin kasa, suka tarwatsa su da barkonon tsohuwa da harsasai masu rai.
Yadda ƴan sanda suka buɗe wuta
Da suke magana da manema labarai, wasu mutum biyar daga cikin masu zanga-zangar waɗanda suka samu raunuka sun soki ‘yan sanda kan abin da suka aikata.
Sun yi ikirarin cewa sai da suka yi tsalle suka faɗa cikin daji lokacin da ‘yan sanda suka buɗe masu wuta da harsasai masu rai.
Yan sanda sun kama ɓata-gari a Kano
A wani rahoton na daban, an ji rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana karin nasara a kan bata-garin da suka saci kayan jama'a yayin zanga-zanga a ranar farko.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kamen bayan jami'an tsaro sun ci gaba da aikinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng