Gwamnatin Yobe Ta Tsugunar da Mutane 2,390, Boko Haram Sun Fatattaki Jama'a
- A dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke gudanar da zanga-zanga saboda matsalolin tsadar abinci da matsalar tsaro, 'yan bindiga sun raba dubban mutane da muhallansu
- Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun matsawa mazauna Mafa da ke karamar hukumar Tarmowa da hari
- Yanzu haka gwamnatin jihar Yobe ta yi kokarin samawa mutanen wurin zama na wucin gadi domin su samu wurin kwana kafin daukar mataki na gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta ceci mutanen karamar hukumar Tarmuwa akalla 2,390 da 'yan kungiyar Boko Haram su ka raba da gidajensu.
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ya Yobe (YOSEMA), Dr. Mohammed Goje ya ce an dauki matakin ne bayan miyagun sun farmaki kauyen Mafa.
Ta'adin Boko Haram a jihar Yobe
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dr. Mohammed Goje ya tabbatar da rasuwar mutane biyu a harin da aka kai yankin a kwanan nan a kan yankuna hudu da ke mazabar Mafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce 'yan ta'addan Boko Haram din sun tarwatsa gidaje 275 wanda ya kawo jumlatan an raba mutane 2,390 da gidajensu.
"An fara sanarwa jama'a mafaka," Dr. Goje
Babban sakataren YOSEMA, Dr. Mohammed Goje ya ce ta'addanci ya daidaita mutanen da ke yankunan Mafa, Bangaro, Ngoyo da Billiri a karamar hukumar Tarmuwa da ke Yobe.
Ya ce yanzu haka an samawa dubban iyalan da su ka rasa muhallansu mafaka a yankin Babban Gida duk a karamar hukumar ta Tarmuwa, Daily Post ta wallafa.
Babban sakataren ya kara da cewa babban abin da su ka sa a gaba a halin yanzu shi ne samawa mutanen abinci da sauran kayan bukatu.
'Yan Boko Haram za su farwa jama'a
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Yobe ta bankado shirin wasu 'yan kungiyar Boko haram ya kai hari kan masu zanga-zangar kwanaki gobe da 'yan jihar za su shiga.
Rundunar 'yan sandan jihar ce ta bayyana cewa akwai bayanan sirri da su ka tabbatar mata da cewa miyagun za su kai masu hari, saboda haka ta bayar da mafita a kan su yi taka tsan-tsan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng