Wani Gwamnan Arewa Ya Sake Hana Zanga Zanga, An Sanya Dokar Awa 24 Babu Fita
- Gwamnatin jihar Katsina ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 tare da haramta duk wani nau'i na zanga-zanga da taron jama'a
- Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Jobe ne ya sanar da sanya dokar bayan barkewar rikici sakamakon zanga-zanga
- Gwamnatin jihar ta ba jami'an tsaro umarnin cafke duk wani mutum ko gungun mutane da aka samu sun karya wannan umarni
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Katsina ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 a karamar hukumar Dutsin-Ma da ke jihar.
Hakazalika, gwamnatin ta sanyan dokar hana fita daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 7:00 na safe a ragowar kananan hukumomi 33 na jihar.
An sanya dokar hana fita a Katsina
Wannan umarnin ya biyo bayan barkewar tashin hankula a wasu sassa na jihar sakamakon zanga-zangar yunwa da aka fara yi, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Jobe ne ya sanar da sanya dokar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Hon. Abdullahi Garba Faskari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Malam Faruk Jobe ya kuma sanya dokar hana zanga-zanga da duk wani nau'in taro na jama'a a fadin jihar.
'Yan daba sun kwace zanga-zanga a jihar Katsina
A cewar sanarwar gwamnatin jihar Katsina ta samu rahoton cewa wasu bata gari ne suka kwace zanga-zangar lumanar.
An ce bata garin sun bankado munanan manufofinsu na fasa shaguna da wawashe dukiyar gwamnati da ta 'yan kasuwa a sassan jihar.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta ga ya zama dole ta sanya wadannan matakan domin kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
Bayan haka, gwamnati ta ba jami’an tsaro umarnin su kama duk wani mutum ko gungun jama’a da aka samu sun saba wannan umarni.
Gwamnan Yobe ya sanya dokar hana fita
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita a wasu garuruwa uku bayan da 'yan daba suka kwace zanga-zangar lumana.
Mai Mala Buni ya ce dokar hana fitan za ta shafi yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar inda aka gano 'yan daban na shirin lalata dukiyar gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng