Masu Zanga Zanga Sun Dira Gidan Buhari a Daura, Bayanai Sun Fito Daga Katsina

Masu Zanga Zanga Sun Dira Gidan Buhari a Daura, Bayanai Sun Fito Daga Katsina

  • Masu zanga-zanga sun dira a gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke mahaifarsa a garin Daura
  • Matasan dai sun yi ta waƙoƙi suna nuna rashin amincewarsu da halin matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwar da ake fama da su a ƙasar nan
  • Bayan an samu da ƙyar an shawo kan matasan da suka fara ƙone-ƙone a wuraren, sai suka wuce fadar Sarkin Daura

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun yi dafifi zuwa gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

Masu zanga-zangar waɗanda suke da yawa, sun shiga zanga-zangar #EndBadGovernance da aka fara a faɗin ƙasar nan ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Babban lauya ya ba Tinubu lakanin kawo karshen zanga zangar da ake yi

Masu zanga-zanga sun je gidan Buhari a Daura
Masu zanga-zanga sun dira a gidan Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Masu zanga-zangar waɗanda suka yi yunkurin kutsawa gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun bayyana cewa sun gaji da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kunna wuta a kusa da gidan Buhari

Wani ganau ba jiyau ba, ya bayyana sun kunna wuta a kusa da ƙofar gidan tsohon shugaban ƙasan yayin da suke ta rera waƙoƙi.

A cikin wani faifan bidiyon da aka sanya a shafin X, an nuna matasa suna ta magana da ƙarfi suna cewa 'bama yi', 'bama yi, 'bama yi'.

Da ƙyar aka shawo kan matasan bayan wani mutum ya fito daga gidan Buhari ya yi musu jawabi

A cewar wani shaida, mutumin ya buƙaci matasan da su zaɓi mutum ɗaya daga cikinsu wanda zai yi magana inda za a ɗauka a bidiyo domin a nunawa tsohon shugaban ƙasan.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan an bindige masu zanga zanga har lahira a ranar farko

Daga gidan Buhari, sai fadar Sarkin Daura

Daga nan sai fusatattun matasan suka nufi fadar Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun harbi ɗaya daga cikinsu a ƙafa lokacin da suke ƙoƙarin tarwatsa su amma masu zanga-zangar ba su tsorata ba.

Wani mazaunin garin Daura mai suna Abdulrashid Adamu ya shaidawa Legit Hausa masu zanga-zangar ba su yi komai ba a gidan tsohon shugaban ƙasan, amma sun yi tare wasu hanyoyi a cikin garin na Daura.

Ya bayyana cewa mutane masu yawa ne suka fito zanga-zangar domin nuna adawa da halin da ake ciki.

"Masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi a kan hanya sannan suka ke gidan Buhari amma ba su yi komai ba bayan an ba su haƙuri sai suka juyo."

- Abdulrashid Adamu

Tsohon ministan Buhari ya shiga zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon minista, Solomon Dalung, ya shiga zanga-zangar da matasa ke yi a birnin Jos na jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Hankula sun tashi bayan jami'in tsaro ya harbi kansa

Tsohon ministan matasa da wasannin ya shiga zanga-zangar ne wacce ake gudanarwa kan halin ƙunci da wahalar da ake fama da ita a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng