Zanga Zanga: Tsohon Ministan Buhari Ya Bi Sahun Matasa Wajen Fitowa Kan Titi
- Tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya fito zanga-zangar da matasa suka fara a ƙasar nan
- Solomon Dalung ya fito zanga-zangar ne a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake fama da shi
- Tsohon ministan ya yi kira ga gwamnatoci da su tashi tsaye su magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya shiga zanga-zangar da matasa ke yi a birnin Jos na jihar Plateau.
Tsohon ministan ya shiga zanga-zangar ne wacce ake gudanarwa kan halin ƙunci da wahalar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Mutane sun fito zanga-zanga a Plateau
Jaridar Leadership ta ce dubunnan mutane suka fito zanga-zangar a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar lumanan sun riƙe alluna da kwalaye waɗanda aka yi rubuce-rubucen kira ga gwamnati na ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace.
Solomon Dalung ya yi wajibi
Tsohon ministan ya yi jawabi ga matasan da suka fito domin nuna adawarsu da halin ƙunci da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan, cewar rahotom jaridar New Telegraph.
Solomon Dalung ya buƙaci jami'an tsaro da kada su yi barazana ga masu zanga-zangar domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su ƴancin yin zanga-zangar lumana.
Solomon Dalung, wanda ya yi minista gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya yi nuni da cewa ƴan Najeriya na matuƙar shan wuya.
A cewarsa akwai buƙatar gwamnatoci a kowane mataki da su tashi tsaye domin magance matsalolin da ke addabar ƙasar nan.
Jami'in tsaro ya yi harbi wajen zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu hargitsi a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri bayan wani jami'in hukumar shige da fice (NIS) ya harbi kansa sau uku a ƙafa.
Jami'in ya yi harbin ne bisa kuskure lokacin da yake aikin tare mutanen da suka fito domin gudanar da zanga-zanga.
Asali: Legit.ng