An Shiga Jimami Bayan An Bindige Masu Zanga Zanga Har Lahira a Ranar Farko

An Shiga Jimami Bayan An Bindige Masu Zanga Zanga Har Lahira a Ranar Farko

  • An rasa rayuka a jihar Neja bayan matasa sun fito zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan
  • Aƙalla rayukan mutane shida ne suka salwanta yayin da ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa masu masu toshe hanya
  • Daga cikin mutanen da aka harba har da wani bawan Allah mai suna Yahaya Nda Isah wanda ke tafiya a kan baburinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Aƙalla mutane shida ne rahotanni suka ce sun mutu yayin gudanar da zanga-zanga a jihar Neja.

Wasu mutanen kuma sun samu raunuka a zanga-zangar da ake ci gaba da yi a garin Suleja.

An harbi masu zanga-zanga a Neja
An bindige wasu masu zanga-zanga a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami'an tsaro sun yi harbi a Neja

Jaridar Daily Trust ta ce waɗanda lamarin ya ritsa da su, an kashe su ne a yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da suka kulle wani bangare na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Hankula sun tashi bayan jami'in tsaro ya harbi kansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasinjoji da masu ababen hawa da ke bin hanyar sun kasa wucewa na tsawon sa'o'i saboda toshe hanyar da masu zanga-zangar suka yi. Wasu ƴan sanda da ke wajen sun kasa shawo kan matasan waɗanda suka fi su yawa.

Tsautsayi ya rutsa da wani a Neja

Daga cikin waɗanda aka kashe har da Yahaya Nda Isah, mazaunin titin Hassan Dalatu ne a Suleja.

An bayyana cewa harsashin ya samu Yahaya Isah ne a kan babur ɗinsa a gaban ofishin ƴan sanda na 'Division A' Suleja inda masu zanga-zangar suka taru.

Wani ɗan uwan ​​marigayin ya bayyana cewa kawun nasa yana kan babur ɗinsa lokacin da harsashin da aka harba domin tarwatsa masu zanga-zangar ya same shi a ƙirji inda nan take ya rasu.

Wani matashin mai suna Malam Abu shi ma ya rasa ransa bayan harbin inda nan take ya ce ga garinku nan.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a ƙofar fadar Mai Martaba Sarki

An rasa rayuka wajen zanga-zanga

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an harbe wasu mutane uku a wurin zanga-zangar.

Sannan an harbi wasu mutum biyu a mahaɗar Suleja da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna amma bai iya tabbatar da cewa ko sun mutu.

An rasa rai a Kano yayin zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kashe wani mai suna Ismael Ahmad Musa a yankin Hotoro da ke ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Wanda aka kashen mazaunin Hoto Danmarke ne, kuma ɗan uwansa Mubarak ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng