Zanga Zanga: Yan Daba sun Tare Jama'a, An Raunata 'Yan Jarida a Kano
- Yayin da zanga-zangar lumana ta rikide zuwa ta tashin hankali a Kano, 'yan jarida biyu sun shiga jerin wadanda aka illata
- Ibrahim Ayuba Isa, dan jarida da wata gidan talabijin a kasar nan ya ji rauni a lokacin da 'yan daba su ka tare motar 'yan jarida
- Ahmad Mahmud, shi ma dan jarida ne da gidan rediyo ya bayyanawa Legit yadda wasu masu zanga zanga su ka bi ta kansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - 'Yan jarida a Kano sun shiga barazana yayin da wasu 'yan daba da su ka shiga rigar zanga-zanga su ka fara tare mutane.
Ibrahim Ayuba Isa, wanda ya ke dan jarida ne a Kano da ke daukar rahoto kan zanga zanga ga gidan talabijin TVC ya shaidawa Legit cewa da kyar ya tsira.
Yadda aka tare motar 'yan jarida a Kano
Ibrahim Ayuba Isa ya ce 'yan jarida sun cika mota guda domin daukar labarai a wannan rana, sai 'yan daba su ka tare su a hanyar Sokoto da ke karamar hukumar Nassarawa inda su ka nemi na goro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gabanin su mika masu wani abu, sai daya daga cikin 'yan daban ya buga gora ya fasa gilashin motar har ya ji masa ciwo a wuya da hannu.
Masu zanga zanga sun tare dan jarida
Ahmad Mahmud, dan jarida a gidan rediyon Premier ya shaida mana cewa ya na cikin tafiya a kokarinsa na zuwa wajen aiki ne wasu masu zanga-zanga su ka yi kansa.
Ahmad Mahmud ya ce daya daga cikin masu zanga-zangar da ke cikin adaidata sahu ne ya yi kokarin bi ta kansa yayin da jami'an tsaro su ka koro su, inda ya ji raunuka.
Miyagu: 'Yan sanda sun fadi shirin zanga-zanga
A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta bankado shirin miyagu na yin amfani da lokacin zanga-zanga wajen tayar da hargitsi a fadin kasar nan.
Babban sufeton 'yan sanda na kasa, Olukayode Ogbetokun ya ce sun dade da samun bayanan sirrin shirin miyagun, shi yasa su ka nemi bayanan masu yin zanga-zangar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng