Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga a Kofar Fadar Mai Martaba Sarki

Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga a Kofar Fadar Mai Martaba Sarki

  • Ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga waɗanda suka taru a kofar fadar mai martaba sarkin Bauchi
  • Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun nemi ganawa da sarkin tun da safiyar Alhamis amma ƴan sanda suka hana
  • Zuwa yanzu dai zanga-zanga ta kankama a jihohin Najeriya inda matasa suka fara nuna rashin gamsuwarsu da wasu matakan gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonɓshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Bauchi ta tarwatse yayin da jami'an ƴan sanda suka harba barkono mai sa hawaye kan waɗanda suka fito.

Tun farko dai masu zanga-zangar sun taru ne a ƙofar fadar Sarkin Bauchi, inda suka nemi a yi masu iso domin su gana da mai martaba sarki.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun ci karfin jami'an tsaro, an toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zanga a Bauchi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Kamar yadda Channels tv ta kawo a rahotonta, ƴan sanda sun dakatar da masu zangar-zangar tare da hana su ƙarisawa cikin fadar sarkin Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

Yayin da masu zanga-zangar suka dage sai sun gana da Sarkin, da nan ne ‘yan sanda suka fara harba barkonon tsohuwa mai sa hawaye domin tarwatsa su.

Gungun matasan sun nananata cewa ya kamata a bari su ci gaba da zanga-zangar wadda suka fara yau Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024.

Harkoki sun tsaya cak yayin da matasa suka fara zanga-zangar da aka daɗe ana jira kan manufofin gwamnati mai ci da suka jefa al'umma cikin tsadar rayuwa.

Daga Abuja zuwa Abeokuta, Fatakwal zuwa jihar Legas, duk an rufe bankuna da wuraren kasuwanci saboda fargabar masu zanga zanga.

Kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka na fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar Naira bayan da Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki wasu matakai shekara guda da ta wuce.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun buɗe wuta yayin da masu zanga zanga suka toshe babban titi a Arewa

Zanga-zanga: An harbe-harbe a Minna

A wani rahoton kuma jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a lokacin da suka yi yunkurin toshe babban titi a Minna, babban birnin jihar Neja.

An dai jiyo karar harbe-harben bindiga da matasan suka matsa sai sun toshe titin bayan sun fara zanga-zanga yau Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262