Gwamna Ya Ballo Aiki, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi Wa Gwamnoni
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya haɗa takwarorinsa gwamnoni da aiki bayan ya ba ƴan Najeriya shawara
- Ya buƙaci ƴan Najeriya da su tambayi gwamnoninsu abin da suke yi da kuɗaɗen da suke samu daga asusun gwamnatin tarayya
- Gwamna Sule ya yi nuni da cewa kuskure ne a ɗora alhakin halin da ake ciki a ƙasar nan kan gwamnatin tarayya kaɗai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su tambayi gwamnoninsu kan ƙarin kuɗaɗen shiga da suka samu daga asusun gwamnatin tarayya.
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa mutane na ji a jika inda ya buƙace su da su tambayi gwamnoninsu abin da suke yi da kuɗaɗen da suke samu daga gwamnatin tarayya, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
Wace shawara Gwamna Sule ya ba da?
Gwamna Sule ya yi nuni da cewa bai kamata a ɗora alhakin halin da ake ciki kan gwamnatin tarayya ba, ya kamata jama'a su ji ba'asi daga wajen gwamnoninsu kan abin da suke yi da kuɗaɗen da aka ba su.
"Lokuta da dama mutane suna duba wasu daga cikin matakai masu tsauri da shugaban ƙasa ya ɗauka kan tattalin arziƙi. Wannan shi ne tsarinsa. Matakai biyu da aka ɗauka suka kawo wannan wuyar da ake sha."
"Na farko shi ne cire tallafin man fetur sannan na biyun shi ne sakin Naira sakaka. Waɗannan matakan su ne waɗanda jama'a ke ta ƙorafi a kansu."
"Mutane na ta tambaya ina kuɗaɗen suke. Kuɗaɗen suna nan. Ana bayar da su ne ga wasu mutane da wurare sannan suna zuwa hannun mutane ta hanyoyi daban-daban."
- Gwamna Abdullahi Sule
Gwamnatin Tinubu ta yi roƙo kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya ƙara fitowa ya roki ‘yan Najeriya da su ƙauracewa zanga-zangar yunwa da ake shirin yi a fadin kasar nan.
Sanata Akume ya yi wannan roko da ake ganin kusan shi ne na ƙarshe gabanin fara zanga-zanga gobe Alhamis a taron manema labarai a Abuja.
Asali: Legit.ng