Sufetan 'Yan Sanda Ya Fadi Shirin da Miyagu su ka Yi Yayin Zanga Zangar Lumana

Sufetan 'Yan Sanda Ya Fadi Shirin da Miyagu su ka Yi Yayin Zanga Zangar Lumana

  • Babban sufeton 'yan sanda na kasa, Olukayode Ogbetokun ya bayyana cewa sun bankado shirin tayar da hargitsi yayin zanga zanga
  • Olukayode Ogbetokun ya bayyana cewa wannan ya sa su ka nemi bayanan jagororin masu gudanar da zanga zangar a fadin kasar nan
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa wasu daga ketare ne su ka dauki nauyin zanga-zanga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Babban sufeton 'yan sandan kasa, Olukayode Ogbetokun ya ce bayanan sirri sun bayyana cewa wasu tsageru sun shirya tayar da hargitsi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Tinubu sun yi kishiyar zanga zanga a Kano, su na goyon bayan gwamnati

Sufeta Janar na 'yan sandan ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, ya ce an gano ana shirin kai hari cikin kasuwanni da lalata kadarorin gwamnati.

Police
'Yan sanda sun fadi yadda wasu ke neman kawo hargitsi a zanga-zanga Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Zanga-zangar lumana ko barna?

Jaridar Vanguard ta wallafa Olukayode Ogbotokun ya ce tun asalin sunan da aka sanyawa zanga-zangar ya nuna cewa ba ta lumana ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa bayanan sirri sun kara tabbatar masu da munanan manufofin masu shirin gudanar da zanga-zangar.

"Mun nemi zama da masu zanga-zanga," IGP

Babban sufeton 'yan sandan kasar nan, Olukayode Ogbetokun ya ce sai da su ka nemi zama da wadanda su ka shirya zanga-zanga a kasar nan.

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa sun so zama da wadanda su ka shirya zanga-zangar domin tabbatar da an san inda aka sa a gaba a kan zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10: Lauya ya nemi alfarma, ya roki masu zanga zanga su rage tsawon lokaci

Ya kuma bayyana cewa sun bukaci bayanan masu shirya zanga-zangar saboda a samu saukin kare rayuka da dukiyoyin masu shirin fita.

Zanga-zanga: Ana daukar matakin dakile miyagu

Rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana cewa ta na kokarin dakile bata-gari daga shiga cikin zanga-zangar.

Olukayode Ogbetokun ya bayyana cewa sun dauki matakin ne domin kare rayukan jama'a.

An fadi masu daukar nauyin zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce wasu mutane daga kasashen ketare ne su ke tunzara jama'a domin gudanar da zanga-zanga.

Amma duk da cewa an gano masu daukar nauyin zanga-zangar, shugaban kasar bai bayyana sunayen wadanda ake da tabbacin sun dauki nauyin zanga-zangar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.