Ana Kukan Babu Kudin Karin Albashi, Gwamnan APC Ya Nada Hadimai Kusan 200
- A jiya Laraba, 31 ga watan Yuli, Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya dauki sababbin hadimai kimanin mutum 160
- Hadiman da gwamnan ya dauka za su taimaka masa ne a harkokin ilimin bai daya, ilimin gaba da sakandare da kuma harkar lafiya
- Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Bala Ibrahim ne ya fitar da sanarwar tare da fadin muƙamin da aka ba wadannan mutanen
- Hakan yana zuwa ne a lokacin da wasu gwamnoni ke kukan ba za su iya kara albashi ba, a Jigawa ba a fara tattaunawa kan karin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da ɗaukan hadimai mutum 166 domin taimakawa gwamna Umar Namadi.
Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Bala Ibrahim ne ya fitar da sanarwar a jiya Laraba, 31 ga watan Yuli.
Legit ta tatttaro sunayen mutanen ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Jigawa, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimai kan ilimi mai zurfi a Jigawa
Gwamna Umar Namadi ya dauki hadimai da za su rika taimaka masa a kan sa ido wajen lura da ilimi mai zurfi a Jigawa
Gwamnan ya dauki mutane 51 daga sassan jihar Jigawa domin su taimaka masa a wannan bangaren.
Hadimai kan ilimin bai daya
Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Bala Ibrahim ya tabbatar da cewa gwamna Umar Namadi ya amice da daukar hadimai a bangaren ilimin bai daya.
A wannan ɓangaren, Bala Ibrahim ya ce gwamnatin Jigawa ta amince da ɗaukar mutane 60 da za su taimakawa gwamnan.
Gwamnan Jigawa ya nada Hadimai kan lafiya
Gwamna Umar Namadi ya dauki hadimai kimanin mutum 55 da za su rika tallafa masa wajen saka ido kan harkar lafiya a Jigawa.
Rahotanni na nuni da cewa gwamna Namadi ya zakulo mutanen ne a cikin dukkan ƙananan hukumomin jihar Jigawa.
Namadi ya yi maganar karin albashi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa ya ce har yanzu gwamnatin jihar ba ta yanke adadin da za ta biya a matsayin sabon mafi karancin albashi ba.
Gwamna Umar A. Namadi ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa ba ta ma fara tattaunawa kan ƙarin albashi da ƙungiyar kwadago ta jihar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng