Abin da Gwammoni 6 Suka Faɗa Game da Zanga Zangar da Aka Fara Yau a Najeriya

Abin da Gwammoni 6 Suka Faɗa Game da Zanga Zangar da Aka Fara Yau a Najeriya

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da takawaransa na jihar Filato na cikin gwamnonin da suka fito suka yi magana kan zanga-zangar da aka fara yau
  • Gwamnonin sun gargaɗi matasa su kaucewa tashin hankali domin ba za su lamunci abin da zai ruguza zaman lafiya ba a lokacin zanga-zanga
  • A yau Alhamis, 1 ga watan Agusta, ƴan Najeriya musamman matasa suka fara zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwar a ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamnonin jihohi aƙalla shida sun gargaɗi masu zanga-zanga su guji duk wani abu da zai kawo tashin hankali ko ya ruguza zaman lafiya.

Gwamnonin da suka haɗa da na jihohin Kano, Ekiti, Legas, Ribas, Bauchi da Filato sun bayyana cewa ba za su lamunci tayar da tarzoma a lokacin zanga-zanga ba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10: Lauya ya nemi alfarma, ya roki masu zanga zanga su rage tsawon lokaci

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang da Abba Kabir.
Gwamnoni sun gargaɗi masu zanga-zanga su guji duk abin da zai kawo tashin hankali a ƙasar nan Hoto: Caleb Mutfwang, Abba Kabir Yusuf
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a yau Alhamis, 1 ga watan Agusta, ƴan Najeriya za su fara zanga-zangar da suka shirya yi kan tsadar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da gwamnoni suka ce kan zanga-zanga

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gargaɗi masu shirin amfani da ƴancin zanga-zanga su kaucewa duk wani abu da zai kawo hargitsi a jihar.

Gwamnan Kano yana goyon bayan zanga-zanga

Abba Kabir ya yi wannan kashedin ne yayin ganawa da malamai, sarakuna da ƴan kasuwar jihar Kano ranar Laraba, rahoton Channels tv.

Mai girma gwamnan ya shirya zama da masu zangar-zangar kuma ya kai kokensu Abuja.

Gwamnan Ekiti ya tuna da EndSARS

A nasa ɓangaren, Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya ce Najeriya ba za ta iya jure sake, "rusa tattalin arzikin ta ba," kamar yadda ya faru a zanga-zangar EndSARS.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fito fili ya goyi bayan zanga zanga, ya caccaki 'yan sanda

A jawabin da ya yi kai tsaye, gwamnan ya roƙi mutanen Ekiti su yi taka tsan-tsan kar su faɗa tarkon masu ƙoƙarin aikata ɓarna da sunan nemawa talakawa ƴanci.

Gwamnan Legas ya gargadi mutane

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce duk masu kokarin fakewa da zanga-zangar lumana domin aiwatar da mummunan nufinsu ba za su ci nasara ba, kuma za a hukunta su.

Ya ce zanga-zangar ba za ta ɓatar da matsalolin ƙasar nan cikin kwanaki 10 ba, sai dai ta maida hannun agogo baya a nasororin da aka fara cimmawa.

Gwamnan Ribas ya ce an dauko miyagu

Gwamnan Siminalayi Fubara Ribas ya ce akwai sahihan bayanai da ke nuna cewa an dauko hayar wasu sojoji da ‘yan daba daga waje da sunan zanga-zanga.

A cewarsa, an ɗauko hayar ɓata garin ne domin lalata wasu muhimman kadarori da ababen more rayuwa a jihar kuma gwamnatinsa ba za ta lamunci haka ba.

Kara karanta wannan

Gwamma Abba ya ɗauki mataki kan masu zanga zanga a Kano, ya aika masu goron gayyata

Gwamnan Bauchi ya kawo mafita

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya ce dole ne a dauki matakin gaggawa don biyan bukatun masu zanga-zangar tsadar rayuwa mai taken, 'EndBadGovernance'.

"Mafi akasarin abubuwan da suka fada gaskiya ne domin mutane sun kai wuya ga yunwa a ƙasa," in ji shi.

Gwamnan Filato a kan zanga-zanga

Gwamnatin jihar Filato karkashin Gwamna Caleb Mutfwang ta ce yin wannan zanga-zangar za ta ƙara jawo wahala ne maimakon a samu sauƙi.

Irinsu gwamnan Kaduna sun roki mutanensu yayin da gwamnan Ogun ya aika da gargadi.

Zanga-zanga: IGP ya ɗauƙi mataki

A wani labarin kun ji cewa Babban sufetan ƴan sanda na kasa ya ɗauki zafi kan masu yunƙurin ta da zaune tsaye da ƙone-ƙone a lokacin zanga-zangar da za a yi.

IGP Kayode Egbetokun ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda suka kama da aikata laifi a faɗin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262