'Yan Sanda Sun Bayyana Tagomashin da Masu Zanga Zanga Za Su Samu, Sun Kafa Sharadi

'Yan Sanda Sun Bayyana Tagomashin da Masu Zanga Zanga Za Su Samu, Sun Kafa Sharadi

  • Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta bayyana shirinta na goyon bayan masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a faɗin jihar
  • Kwamishinan ƴan sandan, Funsho Adegboye, ya yi alƙawarin ba su kariyar da ta dace idan suka gudanar da zanga-zangar cikin lumana
  • CP Funsho Adegboye ya gargaɗi masu shirin kawo fitina da su shiga taitayinsu domin za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta yi alƙawarin goyon baya tare da kare masu zanga-zanga a jihar.

Rundunar ta ce za ta yi haka ne matuƙar dai an gudanar da zanga-zangar cikin lumana a jihar.

'Yan sanda za su kare masu zanga-zanga a Edo
'Yan sanda za su raba ruwa da alewa ga masu zanga-zanga a Edo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Me ƴan sanda suka ce kan zanga-zanga?

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun sha sabon alwashi kan zanga zanga bayan nasarar gwamnati a kotu

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin ranar Laraba, kwamishinan ƴan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya ce ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa za a ba mutanen da ba za su shiga cikin zanga-zangar ba damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

"Mun yi taro da wasu jagororin zanga-zangar, mun amince cewa dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali, za mu kare su amma ba za a tare hanya ba ko tashin hankali."
"Ƴan sanda za su kare su da tallafa musu da ruwan leda da alawoyi. Mun amince cewa za su tsaya ne kawai a dandalin Kings Square, inda a nan za a gudanar da zanga-zangar."

- Funsho Adegboye

Kwamishinan ƴan sandan ya gargaɗi masu shirin tayar da hankali da su nisanta kansu daga zanga-zangar, yana mai cewa za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fito fili ya goyi bayan zanga zanga, ya caccaki 'yan sanda

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

An rufe makarantu saboda zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun jihar ba tare da ɓata lokaci ba.

Umarnin rufe makarantun na zuwa ne gabanin zanga-zangar adawa da taɓarɓarewar tattalin arziki da za a fara ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng