Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Muhimmin Mataki Saboda Zanga Zanga

Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Muhimmin Mataki Saboda Zanga Zanga

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki matakin rufe dukkanin makarantun jihar ba tare da ɓata lokaci ba saboda zanga-zangar da za a gudanar
  • Kwamishinan ma'aikatar ilmi na jihar ya umarce a rufe makarantun saboda gudun abin da ka iya shafar ɗalibai yayin zanga-zangar
  • An kuma dakatar da jarabawar JLC da ake gudanarwa yanzu haka har sai zuwa wani lokaci mai zuwa a nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun jihar ba tare da ɓata lokaci ba.

Umarnin rufe makarantun na zuwa ne gabanin zanga-zangar adawa da taɓarɓarewar tattalin arziki da za a fara ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

An ɗage zanga zangar da matasa za su fara yau a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Gwamnatin Zamfara ta rufe makarantu
Gwamnatin Zamfara ta rufe dukkanin makarantu a jihar Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin wata takarda da babbar sakatariyar ma'aikatar ilmi ta jihar Zamfara, Barira Bagobiri, ta rabawa shugabannin makarantu, makarantu masu zama kansu da sauran jama'a, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka rufe makarantu a Zamfara?

Barira Bagobiri ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kaucewa duk wata barazanar tsaro da ka iya shafar ɗaliban.

Bagobiri ta ƙara da cewa an dakatar da jarabawar JLC da ake yi yanzu haka, sannan za a sanar da ranar da za a ci gaba da jarrabawar, rahoton Radio Nigeria ya tabbatar.

"Ana sanar da jama’a cewa kwamishinan ma’aikatar ilimi, kimiya da fasaha, Mallam Wadatau Madawaki ya amince da rufe dukkanin makarantu jihar nan ba tare da ɓata lokaci ba a ranar 1 ga watan Agusta 2024."
"An ɗauki matakin ne domin kaucewa duk wata barazana ta tsaro da ka iya shafar ɗalibanmu a kan hanyar zuwa makaranta saboda zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Hukumar kwastam ta fadi yadda za ta gudanar da aikinta

"Hakazalika, an dakatar da jarabawar JLC da ke gudana kuma za a sanar da sabon lokacin ci gaba da ita nan gaba."

- Barira Bagobiri

Gwamnatin Yobe ta rufe makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta umarci a rufe duka makarantun sakandire da firamare.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake shirin farawa daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng