Wani Bam Ya Tarwatse a Teburin Mai Shayi, Mutane Kusan 20 Sun Mutu a Arewa

Wani Bam Ya Tarwatse a Teburin Mai Shayi, Mutane Kusan 20 Sun Mutu a Arewa

  • Sa'o'i kalilan gabanin fara zanga-zanga, wani bom da ake zargin ƴan ta'adda suka dasa shi ya tashi a teburin mai shayi a jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa mutane 19 sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon tashin bom ɗin a kauyen Kawuri
  • Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin Borno kan wannan lamari mai ban takaici

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa wani bom da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram suka dasa ya tarwatse a wurin mai shayi.

Akalla mutane 19 suka mutu sakamakon tashin bom ɗin a kauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno ranar Laraba, 31 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 1, gwamnatin Tinubu ta aike da muhimmin saƙo kan zanga zanga

taswirar jihar Borno.
An rasa gomman rayuka yayin da bom.ya ƙara tashi a jihar Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne kwanaki uku bayan da wasu mahara suka kai hari ofishin ‘yan sanda a garin Jakana duk a karamar hukumar Konduga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bom ya kashe mutane a Borno

Wani jami’in gwamnati daga kauyen ya ce bom din ya tashi ne da misalin karfe 8:05 na dare a teburin mai shayi na yankin, wurin da mutanen kauyen suka saba taruwa a yi hira.

“Babu wanda zai iya faɗin taƙamaiman abin da ya faru, amma muna zargin dasa bom din aka yi, ba harin kunar bakin wake ba ne,"
"Mun ga gawarwakin mutane 19 yayin da wasu da dama da ba a tantance ba suka samu raunuka, yanzu haka masu raunin na kwance a asibiti ana masu magani a Maiduguri," in ji shi.

Wane mataki ƴan sandan Borno suka ɗauka?

Kara karanta wannan

"Muna can muna cin abinci," Shugaban Majalisa ya ta da ƙura kan zanga zanga da ake shirin yi

Duk wani ƙokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, DSP Kenneth Daso, bai yi nasara ba, domin wayarsa ba ta shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar, wanda gwamnati ta sha nanata cewa ɓata gari da ƴan ta'adda na iya amfani da danar, Vanguard ta rahoto.

Ƴan sanda sun kwance bom a Legas

Ku na da labarin yan sanda sun yi nasarar kwance bom a jaka a yankin Ikeja da ke jihar Legas a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce wani mutum a mota mara lamba ne ya jefar da bom din ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262