Gwamnan Arewa Ya Fito Fili Ya Goyi Bayan Zanga Zanga, Ya Caccaki 'Yan Sanda

Gwamnan Arewa Ya Fito Fili Ya Goyi Bayan Zanga Zanga, Ya Caccaki 'Yan Sanda

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci matasa da su gudanar da zang-zanga cikin lumana ba tare da tashin hankali ba
  • Abba wanda ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar ya nuna zai iya shiga cikinta idan har masu zanga-zangar ba su tayar da tarzoma ba
  • Ya kuma caccaki ƴan sandan kan abin da ya kira yadda suke biris da umarninsa idan ya ba da kan wasu abubuwa da suka shafi Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fito ƙarara ya goyi bayan zanga-zanga da za a fara a ranar 1 ga Agustan 2024.

Ya ba masu zanga-zangar lumanan tabbacin samun goyon bayansa tare da shan alwashin tarbarsu da kansa a gidan gwamnatin a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamma Abba ya ɗauki mataki kan masu zanga zanga a Kano, ya aika masu goron gayyata

Gwamna Abba ya goyi bayan zanga-zanga
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci matasa su yi zanga-zangar lumana Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Me Gwamna Abba ya ce kan zanga-zanga?

Gwamna Abba ya nuna goyon bayansa ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ranar Laraba, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya nuna cewa ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga amma ya buƙaci matasa da su gudanar da ita cikin kwanciyar hankali, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"A wajenmu, ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga. Ina son masu zanga-zangar su gudanar da ita cikin taka tsan-tsan saboda wasu ɓata-gari na son yin kutse."
"Idan kuka yi zanga-zangar lumana, zan tarbe ku, sannan idan kuna so, zan shiga cikinku."

- Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba ya caccaki ƴan sanda

Gwamna Abba ya nuna rashin jin daɗinsa ga rundunar ƴan sandan Najeriya, inda ya zarge su da rashin biyayya da kuma rashin bin umarnin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 1, gwamnatin Tinubu ta aike da muhimmin saƙo kan zanga zanga

"Na kasa fahimtar dalilin da ya sa hukumomin tsaro, musamman ƴan sanda, ba za su bi umarninmu ba."
"Lokacin da muka gaya musu su yi wannan ko wancan, za su gaya mana cewa sun samu umarni daga 'sama'."
"Wanene 'saman'? Ni ne babban jami’in tsaro a jiha. Idan kuna da matsala a kan hakan, ku je ku sauya kundin tsarin mulkin Najeriya."

- Abba Kabir Yusuf

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaruruwan mutane a jihar Kano sun fito kan tituna inda suke adawa da zanga-zangar da za a yi a gobe.

Mutanen sun cika titunan birnin ne a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024 domin nuna rashin goyon baya ga zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng