Duk da Katobarar da Ya Yi, Akpabio Ya Sake Neman Wata Bukata Wajen 'Yan Najeriya

Duk da Katobarar da Ya Yi, Akpabio Ya Sake Neman Wata Bukata Wajen 'Yan Najeriya

  • Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan su kai zuciya nesa
  • Shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya yi roƙon ya buƙace su da haƙura da gudanar da zanga-zangar
  • Ya bayyana cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kawo shirye-shiryen da za su amfani ƴan Najeriya nan gaba kaɗan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta buƙaci masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan da su dakatar da shirye-shiryensu domin amfanin al’ummar Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan bayan wani zaman gaggawa da Sanatocin suka yi a Abuja, ranar Laraba.

Akpabio ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri
Majalisar dattawa ta bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce ƙungiyoyi daban-daban na shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 1, gwamnatin Tinubu ta aike da muhimmin saƙo kan zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu zai gyara ƙasa" Inji Akpabio

Sanata Godswill Akpabio ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shekara ɗaya kawai ta yi a mulki amma ta ɓullo da tsare-tsaren da za su amfani ƴan Najeriya nan gaba kaɗan

A bisa hakan ne sai ya buƙaci ƴan Najeriya su ƙara kai zuciya nesa domin sauƙi na nan tafe, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Ya ce abubuwan da Tinubu ya yi irinsu rattaɓa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashin ma’aikata, ba da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi da dai sauransu, za su rage yunwa da fatara a ƙasar nan.

Wace buƙata Akpabio ya nema?

"Majalisar dattawa ta buƙaci masu zanga-zangar da su ƙara ba gwamnati lokaci."

- Sanata Godswill Akpabio

Ya ƙara da cewa, ƙudirorin doka daban-daban da majalisar ta zartar za su taimaka wajen magance ƙalubalen tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fama da shi.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jerin jihohin da za a gudanar da zanga zanga a ranar 1 ga watan Agusta

Majalisa ta yi bincike kan kamfanin Ajaokuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta nemi jin ba'asi kan N4.2bn da aka ware a cikin kasafin kuɗin 2024 a matsayin kuɗin albashin ma’aikata na kamfanin ƙarafa na Ajaokuta.

Kamfanin wanda ya kwashe shekara da shekaru ba ya aiki ana ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe domin biyan ma'aikatansa albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng