Tun Kafin Fara Zanga Zanga, An Yi Baram Baram Tsakanin Jagorori da Shugaban 'Yan Sanda

Tun Kafin Fara Zanga Zanga, An Yi Baram Baram Tsakanin Jagorori da Shugaban 'Yan Sanda

  • A jiya Talata, 30 ga watan Yuli aka yi zama ta yanar gizo tsakanin jagororin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da yan sanda
  • Tattaunawar ta kasance ne domin samo hanyar da za a samu zaman lafiya a lokacin zanga zangar saboda kaucewa tarzoma
  • Rahotanni sun nuna cewa an gaza cimma matsaya tsakanin jagororin zanga zangar da yan sanda kan yawo a titunan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta yi zama da jagororin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa domin tabbatar da tsaro.

Jagororin sun tattauna ne kan yadda za a tabbatar zanga zangar ba ta haifar da tarzoma a faɗin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Jagororin zanga zanga sun cire tsoro sun bayyana kansu ga shugaban yan sanda

Zanga zanga
An gaza cimma matsaya tsakanin yan sanda da masu zanga zanga. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an gaza cimma matsaya tsakanin jagororin da rundunar yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharadin yan sanda ga masu zanga zanga

Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya gindaya sharadin cewa ya kamata zanga zangar ta kasance a wuri ɗaya ba tare da yawo a kan tituna ba.

IGP Kayode Egbetokun ya fadi haka ne saboda kaucewa tashin hankali idan matasan suka fito kan tituna.

Matasa sun ce sai sun fito kan tituna

Daya daga cikin jagororin zanga zangar, Ebun-Olu Adegboruwa ya ce ba su amince da maganar tsayawa a wuri ɗaya da yan sanda suka bukata ba.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Ebun-Olu Adegboruwa ya ce wannan kuma ita ce matsayar mafi yawan jagororin zanga zangar.

Masu zanga-zanga za su bi doka da oda

Ebun-Olu Adegboruwa ya ce za su tabbatar da cewa sun bi doka da oda wajen yin zanga zangar ba tare da kawo tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

An gaida matasa: Muhimman nasarori 3 da barazanar zanga zanga ta samar ga talakawa

Ya kuma shawarci sufeton yan sanda kan maida hankali ga yan daba da za su iya shiga cikin masu zanga zangar domin tayar da fitina.

Gwamna Uba Sani ya yi maganar zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi taron gaggawa da sarakuna, malamai da jami'an tsaro domin dakile zanga zanga.

Gwamna Uba Sani ya fadi abin da ke kawo musu fargaba da yasa suke ƙoƙarin ganin ba a yi zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Kaduna ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng