Zanga Zanga: Hukumar Kwastam ta Fadi Yadda Za Ta Gudanar da Aikinta

Zanga Zanga: Hukumar Kwastam ta Fadi Yadda Za Ta Gudanar da Aikinta

  • Yayin da ƴan ƙasar nan su ka yi barazanar fara zanga-zanga daga gobe Alhamis, hukumar kwastam ta ce ba zai taba aikinta ba
  • Shugaban hukumar da ke kula da tashar jirgin ruwa ta Apapa, Babatunde Olomu ya ba wa abokan huldarsu tabbacin haka
  • Shugaban ya ce ya zama dole su kwantar da hankalin masu shigowa da fitar da kaya daga ƙasar nan zuwa kasashen ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Hukumar kwastam ta bayyana cewa zanga-zanga da ƴan Najeriya ke shirin gudanarwa ba za ta dakatar da aikinta a tashar jirgin ruwan Apapa ba.

Wasu fusatattun ƴan kasa sun ware kwanaki 10 na farkon watan Agusta domin gudanar da zanga-zangar kin manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta shata layi, ta hana masu zanga zanga zuwa wasu wurare idan an fito titi

Apapa
Hukumar kwastam ta ce zanga-zanga ba za ta shafi aiki a tashar Apapa ba Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta tataro cewa shugaban hukumar kwastam da ke kula da tashar Apapa a Legas, Babatunde Olomu ya ce za su ci gaba da ayyukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an kwastam za su fito aiki ana zanga-zanga

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar kwastam ta kwantar da hankalin masu safarar kaya zuwa Najeriya da fita da shi zuwa kasashen waje.

Shugaban hukumar da ke kula da tashar ruwa ta Apapa, Babatunde Olomu ya ce akwai bukatar ba abokan hulɗar kasar nan tabbacin za a ci gaba da aiki.

Mista Olomu ya jaddada cewa jami'ansu za su fito domin gudanar da aiki kamar yadda aka saba, ba tare da tsaiko ba.

Zanga-zanga: 'Yan Sanda sun yaba matsayar kwastam

Rundunar yan sanda kasar nan ta godewa hukumar kwastam kan matsayarta na ci gaba da aiki duk da zanga-zanga da za a fara a ranar Alhamis. Kwamishinan 'yan sanda mai kula da rundunar shiyyar tasoshin ruwa ta Yamma, Lanre Ishola ya ce za su mutunta dukkanin ƴancin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan daban Legas sun marawa gwamnati baya, sun yi barazana ga masu shirin zanga zanga

Majalisa ta nemi a fasa zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa majalisar wakilai ta roki ƴan Najeriya su hakura da batun fita tituna domin gudanar da zanga-zanga daga 1-10 Agusta, 2024.

Shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas ne ya yi rokon a ranar Litinin, inda ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bukatar lokaci domin gyara kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.