'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sake Dasa Bam, Ya Hallaka Babban Jami'in Gwamnati a Borno
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun dasa wani bam a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa wanda ya jawo asarar rai
- Wani babban akanta a ƙaramar hukumar Damboa ya rasu yayin da wasu mutane da dama suka samu raunuka a yayin harin
- Harin bam ɗin na zuwa ne ƴan kwanaki bayan wasu mata ƴan ƙunar baƙin wake sun hallaka mutane 42 a Gwoza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wani bam da ake zargin ƴan ta’addan Boko Haram ne suka binne, ya kashe Shettima Mustapha, babban akanta na sashen ilimi na ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno.
Bam din ya kuma jikkata wasu mutane yayin da motar da suke ciki ta taka shi lokacin da suke tafiya.
Yadda bam ya kashe akanta a Borno
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da sojoji da wasu jami’an tsaro ke rakiyar ɗaruruwan motoci da matafiya daga Damboa zuwa Maiduguri, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fashewar ta auku ne kusan wata ɗaya bayan wasu mata ƴan ƙunar baƙin wake sun kashe mutane 42 tare da raunata wasu kusan 100 a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani makusancin marigayin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya yi alhinin rashin da suka yi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Ina matukar baƙin cikin sanar da ku rasuwar Shettima Mustapha, a wani mummunan tashin bam a hanyarsa daga Damboa zuwa Maiduguri ranar Talata."
"Mun yi matuƙar baƙin ciki da wannan rashi, kuma muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da kuma ƴan uwansa. Allah ya jiƙansa ya sa ya huta."
- Wani na kusa da marigayin
An yi jana'izar wanda bam ya kashe
Wata majiya mai tushe ta ce an binne gawar marigayin a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Sauran waɗanda suka jikkata na samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba a birnin Maiduguri.
Ƴan Boko Haram sun farmaki ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
A yayin harin mayaƙan na oko Haram sun kashe jami'in 'yan sanda da wata mata tare da kuma kwashe mayakamai da alburusai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng