Tsadar Rayuwa: Jerin Kasuwancin da Za Su Gamu da Tangarda a Lokacin Zanga Zanga

Tsadar Rayuwa: Jerin Kasuwancin da Za Su Gamu da Tangarda a Lokacin Zanga Zanga

Matasan Najeriya sun shirya fita kan tituna domin nuna fushinsu da adawa da manufofin gwamnati mai ci da suka jawo tsadar rayuwa da yunwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kamar yadda rahotanni suka nuna za a yi wannan zanga-zanga ne tsawon kwanaki 10, daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024.

Matasan Najeriya.
Jerin kasuwancin da zanga-zangar da ake shirin yi za ta fi shafa a Najeriya Hoto: Contributor
Asali: Twitter

Ana yi wa gwamnati zanga-zanga a Najeriya

Gwamnatin Najeriya karƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta roki masu shirya zanga-zangar nan a lokuta daban-daban su haƙura su janye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton da Daily Trust ta wallafa ranar Litinin bayan taron majalisar zartaswa, gwamnatin tarayya ta nanata cewa babu sauran bukatar zanga-zanga saboda ta magance galibin koken matasa.

Kara karanta wannan

Ana fargabar miyagu za su shiga zanga zanga, an samu hanyoyi 5 domin kare kai

To sai dai duk da haka matasa sun kafe cewa zanga-zanga babu fashi duk da kiraye-kirayen Malaman Musulunci, sarakuna da sauran manyan mutane a kasar nan.

Kasuwancin da zanga-zanga za ta taba

A wannan babin Legit Hausa ta tattaro muku wasu sana'o'i da wannan zanga-zanga za ta shafa, ga su kamar haka:

1. Sufuri

Ga dukkan alamu wannan zanga-zanga da aka shirya yi za ta tsayar da harkokin sufurin motoci cak a faɗin Najeriya.

Yayin ganawar masu shirya zanga-zangar da babban sufetan ƴan sanda na ƙasa (IGP), sun nanata cewa za su hau kan tituna, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Idan hakan ta faru, masu sana'o'i kamar direbobin motocin haya, ƴan adaidaita sahu da ƴan acaba za su fuskanci babban ƙalubale a lokacin zanga-zanga.

2. Ƙananan 'yan kasuwa a shago

Haka nan ana hasashen zanga-zanga za ta shafi masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i domin mafi akasari suna rufe wuraren kasuwancinsu ne saboda gudun matsala.

Kara karanta wannan

Abin da gwammoni 6 suka faɗa game da zanga zangar da aka fara yau a Najeriya

Idan ba ku manta ba, hedkwatar tsaro ta gargadi masu motoci, wayoyi da sauran kananan abubuwa masu mihimmanci su yi taka tsan-tsan a lokacin zanga zanga.

Hakan ya sa da yawa daga cikin masu kananan shaguna, masu caji, da masu sayar da wayoyin hannu sun ce ba za su fito ba har sai sun ga yadda ta kama.

Wani mai siyar da wayoyi a bakin titin zuwa Malumfashi, Abubakar Nakowa ya ce ba zai buɗe shagonsa a karon farko ba sai ya ga abin da aka yi a ranar farko.

3. Manyan kantuna

Manyan kantunan siyayya sun fara ɗaukar matakan tsaro domin gujewa abin da ka iya zuwa ya dawo yayin da wasu kuma suka ce ba ma za su fito aiki ba.

Da yake hira da Businessday, wani ma'aikacin kantin sayayya a Legas ya ce ko kaɗan ba su da shirin rufe kantin saboda zanga zanga.

Babban kantin Adeniran Ogunsanya Shopping Mall da ke yankin Surulere ya tabbatar da zai ci gaba aiki, sai dai sun ɗauki matakin tsaro don gudun maimaita abin da ya faru a EndSARS.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10: Lauya ya nemi alfarma, ya roki masu zanga zanga su rage tsawon lokaci

4. Bankunan kasuwanci

Bankuna na ɗaya daga cikin kasuwancin da ake tsammanin zanga-zangar za ta shafa saboda rashin sufuri da kuma yiwuwar tada zaune tsaye.

Duk da ba su sanar da rufe ayyukansu saboda zanga-zanga ba, amma ana ganin toshe hanyoyin da aka shirya yi zai tsayar da harkokin bankuna cak.

Gwamnati ta nemi a bar zanga-zanga

A wani rahoton kuma, Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya roƙi ƴan Najeriya sun gujewa zanga zangar da aka shirya yi a watan Agusta.

Sanata Akume ya tabbatar wa al'umma cewa wannan wahalar da ake ciki ba za ta dawwama ba, nan gaba kaɗan za a ji daɗi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262