Ana Harin Zanga Zanga, Gwamnati Ta Ba da Aikin da Zai Lakume N81bn

Ana Harin Zanga Zanga, Gwamnati Ta Ba da Aikin da Zai Lakume N81bn

  • Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal Dare za ta yi gina sabuwar wacce za ta tashi tun daga Magami har zuwa Dansadau
  • Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa aikin gina sabuwar hanayar zai laƙume kuɗi kimanin N81bn
  • Ya ƙara da cewa an amince da ba da kwangilar aikin ne ga kamfanin Dantata and Sawoe a yayin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 108 daga Magami zuwa Dansadau.

Aikin ginin titin hanyar zai laƙume maƙudan kuɗaɗe har kimanin N81bn.

Gwamnatin Zamfara za ta gina titi
Gwamnatin Zamfara za ta gina titin N81bn Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa, gwamma zai rushe sabon gidan gwamnatin biiliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka amince da ba da aikin?

Ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin gina titin ne a taron majalisar zartarwa na jihar wanda Gwamna Dauda Lawal ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, 29 ga watan Yulin 2024.

Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa taron ya kuma tattauna kan wasu batutuwa da suka haɗa da yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2024.

"Aikin gina titin za a yi shi ne domin ɗaukar matakin gaggawa, saboda magance matsalar rashin tsaro da ba da fifiko kan jin daɗin mutanen da ke zaune a yankin."
"Gwamna ya amince da bayar da kwangilar ga kamfanin Dantata and Sawoe Construction, saboda kasancewarsa wanda ya buƙaci kuɗi kaɗan da sanya lokaci mafi ƙaranci na kammala kwangilar cikin wata 18 bisa kuɗi N81,189,223,505.73."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

- Sulaiman Bala Idris

Gwamnatin Zamfara za ta gina tashar mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fitar da Biliyoyin Naira domin gina tashar motar zamani a Gusau.

Majalisar zartarwar jihar ta amince a fitar da N4,854,135,954.53 domin samar da tashar mota ta zamani irinta ta farko a jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng