An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga sun Farmaki 'Yan Sanda a Shingen Bincike

An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga sun Farmaki 'Yan Sanda a Shingen Bincike

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan jami'an ƴan sanda a shingen bincikensu a birnin Owerri
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka jami'an ƴan sanda huɗu tare da wata budurwa mai sana'ar POS da ke kusa da wajen
  • Rundunar ƴan sandan Imo da ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ɗora alhakin kai harin kan ƴan ta'addan ƙungiyar IPOB

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda mutum huɗu a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Litinin, a kan hanyar Owerri-Onitsha a birnin Owerri, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ana shirin anga zanga, ƴan bindiga sun yi garkuwa da fitaccen sarki a Arewa

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sanda a Imo
'Yan bindiga sun hallaka 'yan sanda hudu a jihar Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Wani mai shago a yankin mai suna, Tony Onwumelu, ya shaidawa jaridar Premium Times cewa ƴan bindigan sun farmaki ƴan sandan ne a wajen shingen bincikensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Eh tabbas ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda a wajen shingen bincikensu kusa a otal ɗin Blossom inda suka hallaka mutum huɗu daga cikinsu."
"Sun kuma yi harbi kan mutanen da ke wucewa amma wata budurwa ce kawai mai sana'ar POS a wajen ta rasu."

- Tony Omwumelu

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da aukuwar lamarin, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa ƴan ta'addan ƙungiyar IPOB ne suka kai hari kan jami'an tsaron.

Kara karanta wannan

Kebbi: An rasa rai bayan 'yan bindiga sun farmaki jami'an hukumar kwastam

Henry Okoyo ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Aboki Danjuma, ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin mummunan kisan kai.

Ƴan bindiga sun farmaki jami'an kwastam

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai farmaki a wani sansanin jami'an hukumar Kwastam a a garin Koko cikin jihar Kebbi.

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka jami'in hukumar mutum ɗaya tare da yin awon gaba wani jami'in, yayin da suka lalata kayayyaki a sansanin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng