Gwamnati ta Shata Layi, ta Hana Masu Zanga Zanga Zuwa Wasu Wurare Idan An Fito Titi

Gwamnati ta Shata Layi, ta Hana Masu Zanga Zanga Zuwa Wasu Wurare Idan An Fito Titi

  • Gwamnatin tarayya ta kara daukar matakin tabbatar da an bi doka da oda yayin zanga-zanga a fadin kasa
  • Gwamnatin ta yi gargadin cewa kai hari irin wadannan wurare zai iya jawo tabarbarewar doka kuma babbar barazana ce
  • A ranar 1 Agusta, 2024 ce ranar da za a tsunduma zanga-zangar gama gari saboda matsalar matsin rayuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gargadi masu shirin zanga-zanga su kaucewa zuwa kusa da gidajen gyaran hali da tarbiyya a fadin kasar nan

Gwamnatin tarayya ta ce ba ta amince masu zanga-zangar lumanar su je ko kusa da dukkanin gidajen gyaran hali 256 da ake da su a kasar ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Tinubu
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta hori masu zanga-zanga su kiyaye da zuwa gidajen yari Hoto: Halliru Nababa
Asali: Facebook

Ban da zuwa kurkuku ana zanga-zanga

Jaridar Punch ta wallafa cewa tuni aka samar da jami'ai Da ke shirin kar -ta-kwana domin hana afkuwar kalubalen da aka fuskanta a lokacin EndSARS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin zanga-zangar EndSARS, an yi kiyasin daurarru kusan 2000 ne su ka tsere daga gidan gyaran hali a Edo da Ondo.

"Ban da hari gidajen gyaran hali," Gwamnati

Shugaban hukumar gidajen gyaran hali da tarbiyya na kasa, Halliru Nababa ya ce ba za su saurarawa duk wanda ya kai hari gidajen ba. Wannan na kunshe ne ta cikin sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abubakar Danlami Umar ya fitar a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban hukumar ya kara da neman hadin kan 'yan Najeriya wajen hada hannu wajen tsare rayuka da dukiyoyin gwamnatin yayin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Minista ya fara ganawa da matasa, Nyesom Wike zai dakile zanga zanga a Abuja

Gwamnati ta nemi a dakata da zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ba wa 'yan Najeriya su yi hakuri, su janye batun tsunduma zanga-zangar gama gari da za a fara ranar Alhamis, 1 Agusta, 2024.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayar da shawarar, tare da bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na kokari sosai domin kawo gyara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.