Asiri Ya Tonu: An Kama Boka da Ake Zargin Yana Tsafi da Kashin Ɗan Adam

Asiri Ya Tonu: An Kama Boka da Ake Zargin Yana Tsafi da Kashin Ɗan Adam

  • Asirin wani boka mai maganin gargajiya ya tonu yayin da aka kama shi dauke da kasusuwan sassan jikin ɗan Adam
  • Bokan ya bayyana abin da yake aikatawa da kasusuwan da kuma wanda ya ba shi su daga jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya
  • Kakakin yan sanda a jihar Anambara, SP Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin tare da faɗin halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambara - Dubun wani boka da yake tsafi da ƙasusuwan mutane ta cika yayin da jami'an tsaro suka cafke shi.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin mai suna Ezekiel ya tabbatar da yana aiki da kasusuwan wajen hada magani.

Kara karanta wannan

"Da Tinubu bai ci zaben 2023 ba," Minista ya fadi halin da Najeriya za ta shiga

Yan sanda
Yan sanda sun kama boka a Anambara. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda a jihar Anambara ta tabbatar da cafke mutumin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama boka da kashin dan Adam

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun kai samame ne gidan da Ezekiel ke ba mutane magani.

Hakan kuma bayan sun samu bayanan sirri ne kan cewa yana amfani da sassan jikin ɗan Adam wajen yin tsafi.

Boka ya amsa laifinsa a Anambara

Jaridar Tribune ta wallafa cewa yayin da ke yi wa Ezekiel tambayoyi ya tabbatar da cewa yana amfani da kasusuwan dan Adam ne wajen hada magani mai karfin gaske.

Sai dai ya bayyana cewa wani dan uwansa ne ya kawo masa kasusuwan daga jihar Ebonyi a wani gari da ake rikicin kabilanci.

Yan sandan sun yi gargadi

Kakakin yan sanda a jihar Anambara, SP Ikenga Tochukwu ya ce yanzu haka suna rike da Ezekiel ana cigaba da bincikensa.

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Tinubu ya dawo biyan al'umma tallafi, an ci moriyar arzikin kasa

Rundunar ta kuma gargadi al'umma kan yin taka tsantsan da jama'a da kuma sanar da ita duk wani motsi na miyagun mutane.

An kama matsafi a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Delta sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da dama tare da wasu matsafa a yankuna daban daban na jihar.

Ana zargin yan bindigar da aka kama da yawaita ayyukan ta'addanci a yankunan Warri, Ugheli, Sapele da sauran wurare a fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng