Gwamna Ya Rufe Makarantu, Ya Fara Ɗaukar Matakai Kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi
- Gwamnatin jihar Yobe ta umarci rufe duka makarantun firamare da sakandire na jihar saboda zanga-zangar da ake shirin yi
- Kwamishinan ilimi a matakin farko, Abba Idriss Adam ne ya sanar da haka a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas
- Matasan Najeriya sun shirya yin zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta a faɗin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta umarci a rufe duka makarantun sakandire da firamare a faɗin jihar daga gobe Laraba.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake shirin farawa daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024.
Wannan umarni na rufe makarantun na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan ilimi a matakin farko da sakandire, Abba Idriss, ya fitar a Damaturu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, sanarwar na ɗauke da sa hannun daraktan sashin gudanar da makarantu, Bukar Modu a madadin kwamishinan.
Gwamna ya ba makarantu hutu saboda zanga-zanga
Bukar Modu ya ce:
"Mai girma kwamishina, Abba Idriss Adam ya umarce ni na sanar da ku cewa ku rufe duka makarantun sakandire da firamare da ke faɗin jihar Yobe.
"Don haka ana umartar kowace makaranata ta ba ɗalibai hutu a ranar 31 ga watan Agusta, 2024 maimakon 2 ga watan Agusta, 2024 da aka tsara a baya."
Hutun zai kare bayan zanga-zanga
Sanarwar ta kara da cewa hutun zai kare a ranar 15 ga watan Satumba, 2023 kuma ana sa ran kowace makaranta za ta dawo ta ci gaba da harkokin ilimi, rahoton Daily Trust.
Ƴan Najeriya musamman matasa sun shirya gudanar da zanga-zangar lumana da zimmar nuna adawa da manufofin gwammati mai ci da suka jefa mutane cikin wahala.
Ɗaya daga cikin jagororin haɗa zanga-zanga a Yobe wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa sun haƙura, ba za su fita zanga-zangar ba.
Ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gayyaci wasu daga cikinsu kuma a zahirin gaskiya da wuya a yi zanga-zanga a jihar Yobe.
"Ka san jihar Yobe ƙaramar jiha ce kuma galibin mutanen cikinta suna tsoron gwamnati, mun fara shirye-shirye to amma jami'an tsaro sun kira wasu daga cikin mu.
"A yanzu dai ina tabbatar maka zai wahala gobe Alhamis a yi zanga-zanga a jihar Yobe, dukkan mu mun saduda," in ji shi.
Matasan Arewa sun janye daga zanga-zanga
Rahoto ya zo cewa Matasan kiristocin Arewa sun bayyana cewa ba su da hannu a shirye-shiryen da ake yi na yin zanga-zanga a Najeriya.
Shugaban kungiyar Rabaran Samson Job ya ce ba za su shiga zanga zangar ba saboda nuna godiya da irin muƙaman da Tinubu ya ba kiristocin Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng