Matasan Arewa Sun Canza Shawara, Sun Faɗi Matsaya Kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

Matasan Arewa Sun Canza Shawara, Sun Faɗi Matsaya Kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

  • Matasan kiristocin Arewa sun bayyana cewa ba su da hannu a shirye-shiryen da ake yi na yin zanga-zanga a Najeriya
  • Shugaban kungiyar, Rabaran Samson Job ya ce ba za su shiga zanga zangar ba saboda nuna godiya da irin muƙaman da Tinubu ya ba kiristocin Arewa
  • Ya ce Bola Ahmed Tinubu ya kafa tsarin daidaito da adalci a rabon muƙaman gwamnatin tarayya tsakanin ƙabilun ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Matasa sama da miliyan ɗaya karkashin kungiyar matasan kiristocin Arewa sun tsame kansu daga zanga-zangar da ake shirin farawa ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyaar matasan kiristocin Arewa, Rabaran Samson Job, ya fitar kan zanga-zangar da ake shirin yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashi, bayanai sun fito

Bola Ahmed Tinubu da masu zanga-zanga.
Matasan kiristoci a Arewa sun tsame kansu daga zanga-zangar da ake shirin yi Hoto: @OfficialABAT, @NigerianStories
Asali: Twitter

Ya alaƙanta matakinnsu na ƙin shiga zanga-zangar da manyan kujerun da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ƴan shiyyar Arewa ta Tsakiya, This Day ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa matasan kiristoci suka janye?

A ruwayar Guardian, Rabaran Samson Job ya ce:

"Tun da ya hau mulki, Shugaba Tinubu ya ɗaura ɗamarar warware ƙalubalen tattalin arziki a ƙasar nan."
"Shugaban kasar ya kuma ɗauki manyan muaƙamai kamar sakataren gwamnatin tarayya da babban hafsan tsaron ƙasa ya ba kiristocin Arewa, wanda ba mu yi tsammani ba."

Kungiyar ta ce kin shiga cikin zanga-zangar da ake shirin yi wata alama ce ta nuna godiya ga karamcin da shugaban kasar ya yiwa Kiristocin Arewacin wajen rabon muƙaman gwamnati.

Kungiya ta ce Tinubu ya kafa tsarin adalci

Ta ƙara da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa tsarin adalci da daidaito a tsakanin kabilu daban-daban a wurin nade-naɗen muƙamai.

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal gabannin fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Tinubu waɗanda matasa ke ganin sun jefa al'umma cikin mawuyacin hali.

Gwamna ya gargadi masu shirin zanga-zanga

A wani rahoton kuma, an ji Gwamna Ademola Adeleke ya ja kunnen masu shirin zanga-zanga su guji duk abin da zai kawo tashin hankali a jihar Osun.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da ƴan Najeriya na da ƴancin yin zanga-zanga amma gwamnatinsa ba za ta lamunci a riguza zaman lafiya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262