"Ko a Jiki na," Mawaki Rarara ya Jaddada Goyon Bayansa ga Tinubu Duk da Shan Caccaka

"Ko a Jiki na," Mawaki Rarara ya Jaddada Goyon Bayansa ga Tinubu Duk da Shan Caccaka

  • Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya bayyana cewa ba zai taba daina nuna goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Tinubu ba
  • Ya fadi haka ne a martani kan yadda jama'a ke caccakarsa, musamman bayan ya saki sabuwar waka da ke goyon bayan shugaban
  • Rarara ya kara da cewa Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa wajen kawo gyara a halin da kasar nan ke ciki, kuma za a yi nasara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na kokarin gaske wajen tallafawa 'yan kasa.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

Mawakin na wannan batu ne bayan matasa sun hasala da sabuwar wakar da ya yiwa shugaban kasa domin jaddada goyon baya, har ta kai ga rufe shafinsa na Facebook.

Tinubu
Mawaki Rarara ya ce zai cigaba da goyon bayan Tinubu Hoto: Wazirin Garba Gaya/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa mawaki Rarara ya ce ya na goyon bayan Bola Tinubu ne saboda kyawawan manufofinsa ga ci gaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rarara ya lissafa ayyukan alherin Tinubu

Mawakin APC, Dauda Kahuta Rarara ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu ya gudanar da ayyukan ci gaba da ya kamata a yaba masa a kai.

Rarara ya ce a zamanin shugaban ne aka kafa hukumar ci gaban Arewa maso Yamma da tabbatarwa da kananan hukumomi 'yancinsu, Daily Trust ta wallafa wannan.

Sauran ayyukan da Rarara ke ganin ya dace a yabawa Tinubu a kai sun hada da kokarin magance yunwa da tsaro wanda za a ga tasirinsu.

Kara karanta wannan

An kai 'yan Arewa bango: Matasa sun dauki matakin kawo karshen asusun Rarara a Facebook

"Ra'ayin mutane ba ya damu na," Rarara

Mawaki Kahuta Rarara ya bayyana cewa sukar jama'a a kan yadda ya ke yabon shugaban kasa ba ya, Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi alkawain ci gaba da wayar da kan jama'a bisa yadda shugaban ke kokarin warware matsalolin Najeriya.

Rarara ya saki sabuwar wakar Tinubu

A baya mun ruwaito cewa 'yan Najeriya sun caccaki mawaki, Dauda Rarara bayan ya saki wakar da ke yabon shugaban kasa maimakon ta halin da kasa ke ciki.

Mawakin ya saki wakar ne kwanaki kadan bayan an ceto mahaifiyarsa daga hannun 'yan bindiga, lamarin da ya sa 'yan kasar nan ke mamakin yadda ya ke yabon gwamnatin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.