Tallafin N90bn: Bayan Babatun Gwamnan APC, EFCC ta Gayyaci Shugaban Hukumar Alhazai
- Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta nemi shugaban hukumar aikin hajji, Jalal Arabi ya gurfana gabanta
- EFCC ta nemi shugaban ya ziyarci ofishinta domin jin inda aka kwana a kan tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba wa alhazai
- Wannan na zuwa bayan gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya zargi hukumar alhazan da almundahanar kudin tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta nemi shugaban hukumar aikin hajji na kasa (NAHCON) ya bayyana a gabanta.
Hukumar na bibiyar yadda aka yi da Naira Biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta ce ta tallafawa alhazan kasar nan da shi yayin aikin hajji bana.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa ana sa ran shugaban zai amsa tambayoyi a kan yadda aka raba tallafin ga alhazan kamar yadda gwamnati ta umarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NAHCON zai ziyarci EFCC yau Talata
A yau Talata ne ake jiran isar shugaban hukumar aikin hajji na kasa (NAHOCN), Arabi Jalal ofishin hukumar EFCC domin amsa tambayoyi a kan tallafin alhazai.
Daily Trust ta tattaro cewa EFCC ta ce ta na aikinta ne na bincike, saboda ta ga alamun almundahana a rabon tallafin ga alhazai.
“A EFCC, babu ruwanmu da addini ko kabila, abin da ke da muhimmanci a wurinmu shi ne dakile ayyukan rashawa da zamba a cikin al'umma."
- Majiyar EFCC
A baya an jiyo shugaban NAHCON ya bayyana cewa dukkanin alhazan da su ka biya ta hukumar gwamnati sun samu rangwamen N1.6m.
Bayanin Alhaji Arabi Jalal ya ci karo da matasayar gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.
N90bn: Gwamnan Neja ya caccaki NAHCON
A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya caccaki yadda hukumar aikin hajjin bana (NAHCON) ta tafiyar da aikin hajjin shekarar 2024.
Gwamnan ya bukaci majalisar tarayya ta kafa kwamitin binciken yadda aka yi da tallafin N90bn da gwamnati ta bayar ganin cewa $400 kawai aka ba alhazai a matsayin guzuri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng