Ana Sauran Kwana 2, Zanga Zanga Ta Gamu Gagarumin Koma Baya a Arewa

Ana Sauran Kwana 2, Zanga Zanga Ta Gamu Gagarumin Koma Baya a Arewa

  • Matasan Najeriya sun kara gamuwa da cikas game da shirinsu na fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati da suka jawo tsadar rayuwa
  • Kungiyoyi da dama a Arewacin Najeriya sun sanar da janyewa daga zanga-zangar ranar Litinin saboda abin da suka alaƙanta da barazanar tsaro
  • Sun bayyana cewa sun fahimci zanga-zangar ba za ta haifar da sakamako mai kyau ba face illa da ƙarin wahala ga talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sa'o'i 48 gabanin fara zanga-zangar da aka shirya yi a Najeriya kan tsadar rayuwa da yunwa, kungiyoyi da dama a jihohi daban-daban sun sanar da tsame kansu.

ACAGL tare da wasu ƙungiyoyi 33 da suka shiga suka fita wajen shirya wannan zanga-zangar sun bayyana cewa sun haƙura kuma sun janye.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani dangane da zanga zangar da za a yi a Najeriya

Zanga zangar matasa.
Kungiyoyi da dama sun janye daga zanga-zanga kwanaki biyu gabanin farawa Hoto: Contributor
Asali: Twitter

Kungiyoyi sun hakura da zanga-zanga

Mai magana da yawun ACAGL reshen jihar Kano, Saeed Sulaiman ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya sanar da cewa sun ɗauki matakin janyewa ne saboda haɗarin da suka hango, da kuma illar da zanga-zangar za ta jawo wa takalawa a kasar nan.

Saeed Sulaiman ya ƙara da cewa sun yanke shawarar ne domin ba da fifiko ga tsaron Kano da Arewacin Najeriya baki ɗaya.

Zanga-zanga: Majalisar matasa ta janye

Har ila yau, ƙungiyar majalisar matasan Najeriya ta yi kira ga matasan da su sake duba shirin nasu, maimakon haka su hau teburin tattaunawa domin bayyana kokensu.

Shugabar majalisar, Azeazat Yishawu, ta yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai jiya Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zargi wasu manyan mutane da ɗaukar nauyin zanga zangar da ake shirin yi

Duk da ta aminta da cewa ana cikin wahala amma ta yi gargadin cewa zanga-zangar ba za ta haifar da sakamako mai kyau ba kuma za a iya samun tashin-tashina.

Ƙungiyoyi da dama sun janye zanga-zanga

Bugu da ƙari kungiyar manyan Arewa (ACF), kungiyar GAMA, da kuma IPU sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kaucewa zanga-zangar.

Kungiyoyin al’adun gargajiya guda uku sun yi wannan roko ne a sanarwa daban-daban wadanda aka rabawa manema labarai a Ilorin, jihar Kwara.

Haka nan ƙungiyar ƴan acaba da masu adaidaita NATOMORAS ta gargaɗi ƴaƴanta su guji shiga zanga-zangar da aka shirya yi daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Gwamna ya zargi manya da zanga-zanga

Ku na da labarin Gwamnan Katsina ya yi zargin akwai sa hannun wasu manyan mutane a zanga zangar da ake shirin yi kan taadar rayuwa.

Malam Dikko Raɗda ya ce duk da mutane na da ƴanci amma yana ganin barin wannan zanga-zangar shi ya fi alheri domin gudun a jawo bore.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262