Yadda Za a Bude Layin MTN da Aka Rufe Saboda Matsalar NIN Cikin Sauki

Yadda Za a Bude Layin MTN da Aka Rufe Saboda Matsalar NIN Cikin Sauki

  • Mutane da dama sun shiga damuwa yayin da kamfanonin sadarwa a Najeriya, musamman MTN, Globacom, Airtel da 9mobile suka rufe layukan wayoyi
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da ba su sanya lambar NIN ɗin su ba ne a layukansu aka hana amfani da su
  • Biyo bayan hakan an gano hanya mai sauƙi da mutane za su iya buɗe layukansu da aka rufe sakamakon rashin sanya lambar NIN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan Najeriya da dama sun koka bayan an rufe musu layukan wayoyinsu a ranar Lahadi, 28 ga watan Yulin 2024.

Mutane da dama sun koka a shafukan sada zumunta kan yadda layukansu musamman na MTN da Airtel suka daina aiki.

Kara karanta wannan

Hukumar NCC ta yi magana kan layukan da aka rufe, ta ba MTN, Airtel da sauransu umarni

MTN ya rufe layukan wayoyi
Yadda za a bude layin MTN da aka rufe saboda NIN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin akwai sa hannun gwamnati?

Da yake mayar da martani, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi zargin cewa kamfanonin sun rufe layukan ne saboda zanga-zangar da ke tafe a ranar, 1 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai tsohon hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad a wani rubutu a shafinsa na X ya ce wani babban jami’in gwamnati ya sanar da shi cewa ba su da hannu a lamarin.

Jaridar Businessday ta ruwaito cewa kamfanonin sadarwa sun fara rufe layukan da ba su sanya NIN ba, kwanaki kafin wa'adin ranar, 31 ga watan Yuli da hukumar NCC ta sanya.

Sauƙaƙƙiyar hanyar buɗe layin MTN

Wani mai amfani da shafin X, mai Ọmọọba Adélẹyẹ Tolu @DoublePrince001, ya koka kan yadda aka rufewa mutane layukansu.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, ya bayyana hanya mai sauƙi kan yadda za a buɗe layin MTN da aka rufe saboda rashin sanya lambar NIN.

Kara karanta wannan

MTN sun rufe maka layi? Ga wata hanya mai sauki ta bude layukan da aka rufe

"Ziyarci https://ninlinking.mtn.ng domin buɗe layin MTN cikin sa'o'i 24 bayan an danna *996*NIN# a kan layin.
Na matata ya bude cikin ƙanƙanin lokaci saboda ta taɓa sanya lambar NIN a baya."
"Idan ba a sanya lambar NIN a layin ba, wannan shafin yanar gizon zai taimaka wajen buɗe layin."

MTN sun yi martani

Da suke martani kan lamarin, kamfanin MTN ya fitar da ƙarin bayani kan yadda mutane za su buɗe layukansu.

An kai ƙarar MTN a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kare haƙƙƙn mallaka ta Najeriya (NCC) ta gurfanar da kamfanin MTN da wasu mutane uku da kamfani ɗaya a gaban kotu.

A cikin ƙarar hukumar NCC ta yi zargin cewa waɗanda ake ƙarar, tsakanin 2010 zuwa 2017, sun yi amfani da sautin kidan wakar wani Maleke Idowu Moye ba tare da yardarsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng