Majalisar Tarayya ta Dakatar da Hutu, Za Ta yi Zaman Gaggawa Dab da Fara Zanga Zanga

Majalisar Tarayya ta Dakatar da Hutu, Za Ta yi Zaman Gaggawa Dab da Fara Zanga Zanga

  • Yayin da aka fara gudanar da zanga zanga a wasu jihohin Najeriya, majalisar kasar nan za ta yi zaman gaggawa
  • Majalisar ta sanya ranar Laraba a matsayin ranar da za ta zauna, duk da cewa 'yan majalisar sun tafi hutu har zuwa ranar 17 Satumba, 2024
  • Duk da ba a sanar da ainihin dalilin gudanar da zaman ba, ana ganin ba zai rasa nasaba da zanga-zangar da 'yan kasa su ka shirya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Yayin da 'yan kasar nan su ka fara zanga zanga a wasu wurare, 'yan majalisa sun sa ranar da za su yi taron gaggawa.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ta barke a kusa da Abuja

Wannan na nufin za su dakatar da hutun da su ka tafi na watanni, inda za su dawo a ranar 17 Satumba, 2024.

Majalisa
Majalisa ta kira taron gaggawa Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa duk da ba a fadi ainihin dalilin zaman ba, ana ganin ba zai rasa nasaba da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Tinubu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar tarayya za ta dakatar da hutu

'Yan majalisar kasar nan za su dakatar da hutunsu domin ganawar gaggawa a kan matsalar kasa, Solace base ta wallafa.

Babu ainihin dalilin taron, amma za a yi zaman kwana daya kafin zanga-zangar lumana da 'yan kasar nan su ka kuduri aniyar gudanarwa.

A sanarwar da magatakardar majalisa, Dr. Yahaya Danzaria ya sanyawa hannu, ya bukaci 'yan majalisar su hallara domin tattaunawar gaggawa.

" Bisa umarnin kakakin majalisa, Rt. hon. Abbas Tajuddeen, ya yi umarnin cewa za a yi zama a ranar 31 Yuli, 2024."

Kara karanta wannan

Minista ya fara ganawa da matasa, Nyesom Wike zai dakile zanga zanga a Abuja

"Ana bukatar ayi shirye-shiryen halartar zaman, saboda za a tattauna muhimman batutuwa,"

- Dr. Yahaya Danzaria

Zanga-zanga: 'Yan majalisa sun bayar da shawara

A wani labarin kun ji cewa 'yan majalisar wakilai da su ka fito daga Arewa maso Yammacin kasar nan sun shawarci jama'arsu da kar su shiga zanga-zangar gama gari.

'Yan majalisar sun bayyana cewa yankin ya sha fama da matsalolin tsaro da hare-hare da lalata ababen ci gaban kasa, saboda haka bai kamata a yi zanga-zanga ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.