Sojoji Sun Mamaye Babban Titin Abuja, Sun Ɗauki Mataki Kafin Fara Zanga Zanga

Sojoji Sun Mamaye Babban Titin Abuja, Sun Ɗauki Mataki Kafin Fara Zanga Zanga

  • Dakarun sojojin Najeriya sun mamaye babban titin Abuja zuwa Keffi kwanaki uku gabannin zanga-zangar da ake shirin yi
  • A ƴan makonnin da suka shige, batun zanga-zanger da matasa ke shirin yi kan tsadar rayuwa ne ya fi jan hankali a Najeriya
  • Bisa haka ne sojoji suka kafa shingen binciken ababen hawa a titin Abuja-Keffi, lamarin da ya jawo cunkoso a babban birnin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Matafiya da masu ababen hawan da ke bin titin Keffi-Abuja sun gamu da tsaiko yayin da jami'an tsaro suka mamaye titin yau Litinin, 29 ga watan Yuli.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojoji sun kafa shinge a kan babban titin domin bincikar motocin da za su shiga babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Dakarun sojojin Najeriya.
Sojoji sun kafa shingen binciken ababen hawa a titin Keffi-Abuja ana shirin fara zanga-zanga Hoto: Kola Sulaiman
Asali: Getty Images

Dakarun Sojoji sun tare titi a Abuja

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, sojojin sun tare hanyar ne a daidai barikin Sani Abacha kafin ƙarasawa babban shataletalen AYA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron ba su sanar da shirinsu ba kafin lokacin kuma yanzu haka matakin da suka ɗauka ya haifar da cunkuso.

Binciken da sojojin ke yi yanzu haka ya haifar da dogon cunkoso har zuwa gadar Nyanya, sama da kilomita 12 zuwa shataletalen AYA.

Abuja: Ma'aikata sun koma gida

Rahotanni sun ƙara da cewa ma'aikatan gwamnati da ƴan kasuwa da dama da ke aiki a Abuja na zama ne a wajen birnin a wurare kamar Karu, Nyanya, Maraba da Masaka.

Sai dai sakamakon binciken da sojojin suka fara, bisa tilas da yawansu suka koma gida bayan shafe tsawon lokaci a cunkoso.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa zanga-zangar cire tallafi a mulkin Jonathan ba a samu rigima ba'

Matakin sojojin na zuwa ne sa'o'i 72 gabanin fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa wacce aka shirya farawa daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

TUC ta tsame hannu daga zanga-zanga

A wani rahoton kun ji cewa kungiyar kwadago TUC ta bayyana cewa ba za ta shiga zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta ba.

Shugaban TUC na kasa, Festus Osifo ya ce ba su san wa waye suka shirya zanga-zangar ba kuma babu wanda ya tuntuɓe su kan batun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262