"Tinubu Ba Masihirci Ba ne": Minista Ya Fadi Abin da Ya Dace 'Yan Najeriya Su Yi
- Olabunmi Tunji-Ojo ya yi kira ga ƴan Najeriya su kai zuciya nesa, su ƙara ba shugaban ƙasa Bola Tinubu lokaci domin ya yi gyara a ƙasar nan
- Ministan harkokin cikin gida ya bayyana cewa babu adalci a yi tsammanin cewa Tinubu zai magance matsalolin ƙasar nan cikin ƙanƙanin lokaci
- Ya nuna cewa matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan a yanzu, shugaban kasa Tinubu zuwa ya yi kuma ya gaje su domin dama can sun daɗe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara ba Shugaba Bola Tinubu lokaci domin magance ƙalubalen tattalin arziƙin da ya addabi ƙasar nan.
Ministan ya kuma yi kira ga masu shirin fita zanga-zangar da za a gudanar a ranar 1 ga watan Agusta da su kasance masu kishin ƙasa.
"Tinubu na buƙatar lokaci" - Tunji-Ojo
Olabunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels tv a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai kamata a yi tsammanin cewa Tinubu zai magance matsalar da ta shafe shekara 100 a cikin shekara ɗaya kacal ba.
Jaridar TheCable ta ce ministan ya nuna cewa matsalolin da ake fama da su a yanzu, sun samu ne sakamakon rashin iya gudanar da mulki a cikin shekara 100, 60, 30 da suka gabata.
"A iya abin da na sani, shugaban ƙasa bai taɓa kamfen cewa shi masihirci ne ba, ya yi kamfen ne a matsayin ɗan ƙasa, ya yi yaƙin neman zaɓe ne bisa manufar 'Renewed Hope'".
"Idan ana son gyara abin da ya lalace, ana buƙatar lokaci, kuma muna kan gaɓar yin wannan gyaran."
- Olabunmi Tunji-Ojo
Matsayar ministan a kan zanga-zanga
Olabunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa kamata ya yi duk sai an gama bin hanyoyin tattaunawa domin samun maslaha kafin a fara zanga-zanga.
Ya nanata cewa Tinubu da alheri ya zo kuma ya ɗauki matakai masu kyau ciki har da cire tallafin man fetur wanda ya bayyana a matsayin annoba.
Ministan ya ƙara da cewa a yanzu Najeriya jinya take yi kuma za ta wartsake ta dawo cikin ƙoshin lafiya.
Diyar Tinubu ta magantu kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗiyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, Folashade Tinubu ta yi magana kan shirin zanga-zangar matasa a faɗin Najeriya.
Folashade wacce ta ja kunnen iyaye ta tabbatar da cewa babu wata zanga-zanga da za a yi a jihar Legas a ranar 1 ga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng