Kungiya Ta ba Aliko Dangote Mafita Kan Rikicinsa da Hukumomi a Najeriya

Kungiya Ta ba Aliko Dangote Mafita Kan Rikicinsa da Hukumomi a Najeriya

  • Ƙungiyar Arewa Youth Assembly ta yi magana kan taƙaddamar da ake yi tsakanin Aliko Dangote da hukumomi a Najeriya
  • Ƙungiyar ta buƙaci Dangote da ya bi ƙa'idoji da dokokin hukumomin NMPDRA, NNPCL da NUPRC masu kula da ɓangaren mai
  • Matasan sun bayyana cewa kuskure ne Dangote ya buƙaci a hana ƴan kasuwa lasisin shigo da man fetur a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Arewa Youth Assembly ta ba shugaban matatar man Dangote, Alhaji Aliko Dangote, shawara kan rikicinsa da hukumomi a Najeriya.

Ƙungiyar ta buƙaci Dangote da ya bi ƙa’idoji da dokokin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) a matsayin hukumar da ke kula da masana’antar mai da iskar gas ta ƙasa.

Kara karanta wannan

An maka bankin CBN kara a gaban kotu kan manyan laifuka 3, bayanai sun fito

Dangote ya samu shawara kyauts
An bukaci Dangote ya bi ka'idojin hukumomi a Najeriya Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

An zargi Dangote da nuna son kai

Kakakin ƙungiyar, Mohammed Salihu Danlami, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya ce ya ce zai zama son kai ga Dangote ya sa ran NNPCL zai sauya ƙa’idojin domin faranta masa rai

Mohammed Danlami ya ce kafin kafa matatar mai ta Aliko Dangote, akwai hukumomin NNPCPL, NUPRC, da NMDPRA da aka samar domin gudanar da ayyukansu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Wace shawara aka ba Aliko Dangote?

Danlami ya ce ya kamata Dangote ya fahimci cewa ɓangaren mai da iskar gas na ƙasar nan yana aiki ne bisa dokoki.

"Akwai mamaki cewa Dangote a matsayinsa na ɗan kasuwa, ya manta da cewa dole akwai gasa a cikin harkar kasuwanci."
"Bincikenmu ya nuna cewa yana son hukumar NMDPRA ta ƙi ba kowa lasisi domin shigo da man fetur. Sun gaya masa ko kaɗan hakan ba zai yiwu ba."

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki

"Ya ɓata musu suna sannan yana ƙoƙarin tunzura ƴan Najeriya a kan hukumar NMDPRA, yana iƙirarin cewa suna ba ƴan kasuwa lasisi waɗanda suke shigo da man fetur mara inganci."
"Muna kira ga majalisar tarayya da ta bayyana sakamakon da aka samu daga ɗakin gwaji na matatarsa, domin bayanan da muka samu daga majiyoyi da dama sun nuna cewa man fetur ɗinsa baya da inganci."

- Mohammed Danlami

Karanta wasu labaran kan Dangote

Kwankwaso ya goyi bayan Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran siyasar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi martani kan rigimar Aliko Dangote da hukumar NMDPRA.

Kwankwaso ya gargaɗi gwamnatin tarayya inda ya ce ya kamata ayi mai yiwuwa domin tabbatar da inganta matatar Dangote da ya ci $20bn.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng