Zanga Zanga: 'Yan Sanda Sun Cafke Matashi Mai Kiran Jama'a Su Fito Kan Tituna
- Wani matashi mazaunin garin Suleja a jihar Neja mai suna Wali Haruna ya faɗa hannun ƴan sanda bisa zargin tunzura jama'a
- Matashin dai ya yi rubutu a Facebook inda ya yi kira da a fito zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan daga ranar, 1 ga watan Agusta
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cafke matashin inda ya ce ana ci gaba da yi masa tambayoyi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wani matashi mai suna Wali Haruna, mazaunin Suleja a jihar Neja, ya shiga hannun ƴan sanda kan kiran matasa su fito zanga-zanga.
Wali Haruna ya yi wani rubutu ne a Facebook yana kiran a shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.
Ƴan sanda sun cafke matashi a Neja
Jaridar Daily Trust ta ce ƴan sanda sun yi caraf da shi ne a gidansa da ke unguwar Kabula a Suleja ranar Juma’a kafin a miƙa shi zuwa sashen CID da ke Minna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɗan uwan matashin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rubutun da ya yi ne a shafinsa na Facebook ya sanya aka kama shi, rahoton jaridar Sahara Reporters ya tabbatar.
Ya ce ya yi rubutu a Facebook, yana mai cewa “Za a iya yin zanga-zanga a Najeriya. Muna goyon hakan. Mu je zuwa"
Wadannan da sauran rubuce-rubucen da ya yi ne suka sanya ya faɗa komar ƴan sanda.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cafke matashin wanda ya yi kiran da a fito zanga-zanga.
“An gayyaci Wali Haruna mazaunin Suleja ne a ranar 26 ga watan Yuli, domin amsa tambayoyi bayan ya raba bayanan zanga-zanga a shafukan sada zumunta."
"Ana yi masa tambayoyi ne saboda ana zarginsa da tunzura jama’a su yi zanga-zanga da tabbatar da ko yana cikin wasu gungun mutane da ke shirin yin zanga-zanga da gano yadda za a gudanar da irin wannan zanga-zangar domin a yi taka tsantsan."
- SP Wasiu Abiodun
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
Zanga zanga: Kungiyar Amnesty Intl ta caccaki gwamnati kan kama ɗan gwagwarmayan Tiktok
Shehu Sani ya lissafo hanyoyi 6 da zanga zangar lumana ke komawa tashin hankali
Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki
Ƙungiya ta fice daga shiga zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan asalin jihar Zamfara (ZIEF) ta sanar da janyewa daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanin haƙiƙanin shugabannin da za su jagoranci zanga-zangar a ƙasa baki ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng