Shehu Sani Ya Lissafo Hanyoyi 6 da Zanga Zangar Lumana Ke Komawa Tashin Hankali

Shehu Sani Ya Lissafo Hanyoyi 6 da Zanga Zangar Lumana Ke Komawa Tashin Hankali

  • A yayin da ake shirin fara zanga-zanga a faɗin ƙasar nan, Shehu Sani ya yi magana kan abubuwan da za su iya sanyawa a samu rikici
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya lissafo hanyoyi shida da zanga-zangar lumana ke komawa tashin hankali
  • Shehu Sani ya ce idan jami'an tsaro suka harbi masu zanga-zanga, tabbas rikici yana iya ɓarkewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani, ya yi magana kan abubuwan da ke sanyawa zanga-zangar lumana ta rikiɗe ta koma tashin hankali.

Shehu Sani ya bayyana cewa idan jami'an tsaro ɗauke da makamai suka harbi masu zanga-zanaga, tana iya rikiɗewa ta koma tashin hankali.

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki

Shehu Sani ya yi magana kan zanga-zanga
Shehu Sani ya bayyana hanyoyi shida da zanga-zangar lumana ke komawa tashin hankali Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Shehu Sani ya magantu kan zanga-zanga

Tsohon sanatan ya lissafo abubuwan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi, 28 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman na Shehu Sani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.

An dai shirya gudanar da zanga-zangar ne domin nuna adawa da halin ƙunci da wahalar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan, tare da jawo hankalin shugabanni kan su yi abin da ya dace.

Abubuwan da ke kawo rikici a zanga-zanga

Ga abubuwa shida da tsohon sanatan ya lissafo waɗanda ke sanyawa zanga-zangar lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankali:

  • Jami'an tsaro ɗauke da makamai su harbi masu zanga-zanga da harsashi mai rai
  • Ƴan daba daga cikin masu zanga-zanga su kai hari tare da sace kayayyaki a shaguna, ofisoshi, gidaje da wuraren jama'a
  • Ƴan daban da aka ɗauki nauyi su farmaki masu zanga-zangar lumana
  • Masu zanga-zanga su ƙi bin umarnin shugabanninsu wanda hakan zai sanya a rasa doka da oda.
  • Samun rikici tsakanin ƙungiyoyin da ke zanga-zanga
  • Wasu masu mugun nufi su yi kutse cikin masu zanga-zangar lumana

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Shehu Sani ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba da fifiko wajen duba cancanta yayin naɗa muƙamai.

Shehu Sani ya gargadi shugaban ƙasan da kada ya yi irin kuskuren magabacinsa, Muhammadu Buhari, ya yi a lokacin da yake kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng