Tinubu Ya Rage Albashinsa da Kaso 50% da Soke Ofishin Uwargidansa? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu Ya Rage Albashinsa da Kaso 50% da Soke Ofishin Uwargidansa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Fadar shugaban ƙasa ta ja hankalin ƴan Najeriya kan wani jawabin da yake ta yawo wanda ake cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi
  • A cikin jawabin wanda aka danganta da shugaban ƙasan, Tinubu ya bayyana cewa ya soke ofishin uwargidan shugaban ƙasa domin tsuke aljihun gwamnati
  • Sai dai, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fito a shafinsa na X ya musanta wannan batun

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya yi magana kan batun cewa Shugaba Bola Tinubu ya rage albashinsa da kaso 50%.

Bayo Onanuga ya roƙi ƴan Najeriya da su yi watsi da batun domin babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa daga Arewa sun ba mutanen yankinsu muhimmiyar shawara kan zanga-zanga

Fadar shugaban kasa ta musanta jawabin da aka ce Tinubu yayi
Tinubu bai rage albashinsa ba Hoto: @OgaNlaMedia
Asali: Twitter

Da gaske Tinubu ya rage albashinsa?

Onanuga ya musanta jawabin da ake dangantawa da shugaban ƙasan ne a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jawabin da aka ce Tinubu ya yi, ya bayyana cewa ya ɗauki matakan tsuke aljihun gwamnati domin hana matasa fitowa zanga-zangar da ake shirin yi.

Daga cikin matakan akwai soke ofishin uwargidan shugaban ƙasa da rage albashin da ake ba shi da kaso 50%.

Wane martani fadar shugaban ƙasa ta yi?

A cikin martanin da ya yi, Bayo Onanuga, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da jawabin domin babu ƙamshin gaskiya a cikinsa ko kaɗan.

Ya bayyana cewa ko kaɗan shugaban ƙasan bai rage albashinsa ba, sannan bai soke ofishin uwargidan shugaban ƙasa ba.

"Wannan aikin magauta ne masu son ganin sun kawo ruɗani da hargitsi a cikin ƙasa. Ku yi watsi da shi. Shugaba Tinubu bai yi wani jawabi ba."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jigon APC ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

- Bayo Onanuga

Jigon APC ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC, Uche Nwosu, ya roƙi ƴan Najeriya da su ba Shugaba Bola Tinubu lokaci tare da fasa yin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Uche Nwosu ya bayyana cewa babu adalci ko kaɗan a yi tsammanin cewa gwamnatin da ta yi shekara ɗaya a kan mulki za ta gyara ɓarnar da aka kwashe shekaru ana yi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng